An binne gawar Attajiri a kasar Amurka tare da motarsa kamar yadda yayi wasiyya (Hotuna)
An binne gawar Attajiri a kasar Amurka tare da motarsa kamar yadda yayi wasiyya (Hotuna)
– An binne wani dattijo a kasar Amurka tare da motar sa kamar yadda ya nuna muradi
– Dattijon ya bukaci haka ne sakamakon kaunar motar sa dayake yi
Wani ban al’ajabi ne ya faru a birnin California na kasar Amurka, inda wani mai kudin kauye mai suna Lonnie Hollawaya ya bar wasiyyar idan ya mutu a binne shi tare da motarsa, kuma yana zaune a cikinta.
Lonnie Hollaway mai shekaru 90 ya bar wannan wasiyya ne sakamakon tsananin kaunar motar tasa kwaya daya tio dayake yi, motar ta Lonnie kirar Pontiac Catalina-1973 ce.
Haka kuwa aka yi yayin da yan uwa da abokan arziki suka taru suka sanya masa kayan ado, sa’annan aka sanya shi a kujerar direba tare da bindigoginsa, sa’annan aka binne shi kusa da matarsa da ta rasu shekaru biyu baya.
Lonnie a cikin motarsa
Duba da hoton marigayi Lnnie, zaku ga tamkar yana shirin tuka motar ne, sai dai abin da NAIJ.com bata sani ba shine, kodai an fara tuka mota ne a barzahu.
Ga sauran hotunan a nan:
Lokacin da za’a sanya gawar Lonnie
Lonnie
An shigar da Lonnie
Katafaren kabarin Lonnie
Toh fa! lallai idan da ranka ka sha kallo!