Matsaloli da ake samu idan ankayi kuskure Yin Allura A Dantse
Shanyewa, rauni, sagewa ko ciwo na iya biyo bayan allura a dantse.
Waɗannan matsaloli na faruwa ne idan aka samu kuskure yayin allura a dantse kamar haka:
1. Tsira allura a kan jijiyar laka.
2. Allura na iya haifar da kumburin da zai danne ko shaƙe jijiyar laka.
3. Lahani daga ruwan allura wanda wa’adinsa ya riga ya ƙare, da dai sauransu.
Waɗanda suka fi gamuwa da wannan matsala sun haɗa da:

1. Ƙananan yara, musamman saboda tsoron allura suna yin zille-zille yayin yin allurar ko kuma saboda tsokokin jikinsu ba su gama girma ba.
2. Wanda bai ba da haɗin kai ba yayin allura na iya gamuwa da wannan matsala ko da babba ne.
3. Tsofi, musamman saboda raguwar kaurin tsokokin jiki yayin da shekaru suka fara miƙawa.
4. Mai siririn dantse ko wanda ya rame sosai.
5. Wanda ya faɗa hannu wanda bai ƙware ba.
6. Wanda tsautsayi ya faɗawa, saboda wasu su kan ce “allura ba ta da gwani!”
Daga cikin matsalolin da ke iya ƙara afkuwar matsalar shanyewar hannu ko ƙafa bayan allura, musamman ga yara, akwai al’adar nan ta tsorata yara da yi musu allura idan suna ƙiriniya ko kuma idan ana so su yi ko bar wani abu. Tsorata su da allura yana shiga tunaninsu cewa allura aba ce mai ciwo sosai. Saboda haka, duk lokacin da za a yi musu allura suke tsorata har su fara zille-zille. Hakan kuma na iya sa allura ta sauya hanyarta zuwa jijiyoyin laka.
Idan kana fama da shanyewar hannu, gaza damƙa ko riƙo da hannu, sagewa, zogi ko ciwo bayan allura a dantse, tuntuɓi likitan fisiyo a yau.
Physio Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




