Labarai

Yadda ƴar Najeriya mai kwalin HND ta samu gurbin karatun digirin digir kyauta har 7 a Amurka

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Islamiyat Ojelade, mai kwalin HND ta tsallake duk wani ƙalubale akan hanyar ta inda ta samu gurbin karatu kyauta har guda 7 domin yin digirin digir a ƙasar Amurka. Shafin na LH na wallafa

Islamiyat na da kwalin HND, inda ta karanci  Science Laboratory Technology, a kwalejin kimiyya ta tarayya dake Ilaro. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Masu kwalin HND ba kasafai suke samun wannan damar ba

Za a yi tunanin cewa dole sai Islamiyat ta fara yin digirin digirgir (masters) ko sharar fagen sa, kafin samun wannan damar musamman yadda ake bambanta masu digiri da HND a Najeriya.

Amma abin mamakin shine gurbin karatun na kyauta na digirin digir (PhD) ne, kai tsaye daga HND.

Ga abinda budurwar ta rubuta a shafin LinkedIn ɗin ta:

Duba da bambancin dake akwai a tsakanin digiri da HND a Najeriya, naji tsoro sannan na rasa abinyi bayan na kammala karatu na.

Ina mai farin cikin sanar da ku cewa zan fara karatun digirin digir (PhD) ɗina a fannin Chemistry a jami’ar jihar Florida,  Tallahassee, Florida, a Amurka a wannan kakar mai zuwa, bayan na samu guraben karatu kyauta daga jami’o’i 7 a ƙasar Amurka, da kwalin HND ɗina a fannin Science Laboratory Technology (Chemistry).

Sunayen makarantun da ta samu gurbin karatun na kyauta

Makarantun da ta samu gurbin karatun sune, jami’ar jihar Florida, jami’ar Massachusetts Armherst, jami’ar Kansas, jami’ar Kentucky, jami’ar Texas ta Arewa, kwalejin kimiyya ta Rensselaer, da jami’ar Marquette.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button