Musa L. maje Ya bankado Wani Gardi mai Amfani da sunan Mace a Facebook
Musa L.Maje wanda yayi amfani da sunan Zahra mansur da asirinsa ya tonu kwanan bayyana a yau shima ya yada ɓallin wani matashin saurayi inda shima dubunsa ta cika.
Musa L maje yayiwa wannan matashi mai amfani da sunan saddiqa Aliyu nasiha duba da irin yadda ya shiga hannun hukuma ga abinda yake yiwa dan uwansa nasiha.
“Assalam Alaikum…
Banso nai magana akan abinda yake faruwa ba, ina ankare da komai amma ban cika damuwa da abinda be shafen ba, dafarko nayi kokarin yi masa magana akai, nace masa tunda aikin ya bude ya canza salo, duba da yaron yanada hankali kuma da respecting mutane.

Amma bai dauka ba, jiya nakama sunansa still a banza. Duk da cewa nasamu korafe korafe da dama akan account din.
Duk me mu”amula da wannan account din me suna siddiqa to yana mu’amula ne da wannan yaron me suna abbati wanda shine tsohon me amfani da wani account da shima ya taba shahara Miss Haleema.
Da fatan zamu kiyaye, Sai a rufe chapter haka.
Allah ya kyauta.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





