Wata matar Aure Taje neman Maganin Mallaki Mijinta Reshe ya Juye da Mujiya
Wata Matar aure a jihar Katsina da ke arewacin Nigeriya taje neman maganin mallakar miji inda wani boka sai reshe ya juye da muciya inda garin ta mallake mijinta sai boka ya malake ta.
A wani rahoto da majiyarmu ta samu a cikin wannan faifan bidiyo ya nuna cewa wata matar aure da take aure. Wani mutum mai kudi taje neman magani domin ta mallake shi duk abinda take yayi mata amma sai ana zaton wuta a masaka a kasameta a maje ma ga tattaunawar boka da manema labarai.
” Na sadu da ita wannan tabbas nayi amma dalilin ba ni nemanta nayi ba”
To kai ya matar da tazo neman maganin mallakar mijinta ka mallaketa.
“Wallahi ni ban mallaketa ba”
To gashi ae taki mijinta amma kai gashi ta dafo abinci ta kawo farfesu ta kawo maka
“A’a wallahi ni ba abinda nayi mata”
To kai yanzu malami ni ko me
“Eh, ni malami malamin addini”
Amma kuma kasan zina haramun ce
“Eh nasani ƙaddara ce ta hauni”
Ga yadda tataunawar matar mai suna saratu Ibrahim tayi da manema labarai.
Hajiya ya sunanki ?
“Saratu Ibrahim”
Miye alakar ki da wannan mutum
“Malami na ne, magani naje amsowa gurin shi, shi kuma mijina mai Kudi ne idan nace ya bani kudin biki ko suna baya bani, shine nace bari naje na hada shi da malam.”
To ya ankayi maimakon a samu kan mijin sai anka samu kan malam!?
“Ban san inda matsalar take ba”
To yah Ankayi kike yiwa malam abinci kina kaima?
“Tabbas idan na boye muku bazan boye Allah ba saboda ko yanzu ko anjima zan iya mutuwa ni na nemesa”
Kina girko abinci kina kawo mishi?
“Tabbas ina dafo abinci ina kawo mishi tabbas sau daya ne sai ranar munkayi da shi”
Shin da gaske ke kan gadon mijin ki kwanta da wannan bokan ?
“Haka ne”
Ga Bidiyon nan sai ku saurara.