murna ta koma ciki ! Hukumar PPPRA Ta Maida Farashin Litar Man Fetur Zuwa 212 A Nijeriya
Hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan arzikin mai a Nijeriya, ta tsaida farashin litar PMS wanda aka fi sani da man fetur a kan N212.11.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yi wannan karin kudi ne a ranar 12 ga watan Maris, 2021.
PPPRA ta bada wannan sanarwa ne a jeringiyar farashin kayan mai da ta fitar a wannan watan na Maris. An yi lissafin ne a kan yadda ake shigo da kaya.
Ma’ikatar NPA mai kula da tasoshin ruwa ta na karbar N2.49 a kan kowane lita, bayan haka NIMASA mai lura da hanyoyin ruwan kasar ta na cin N0.23.
Ana kuma karbar N1.61 a matsayin ladar ajiyan gangunan mai, bayan N2.17 da ake karba a matsayin haraji na kowace litar man fetur da ta shigo kasar.
Idan aka yi lissafi, kowace litar fetur da aka tace, za ta tashi a kan N189.61 kafin ta iso kasar nan.
PPPRA ta tsaida kudin sari a kan N4.03, gwamnati za ta karbi N1.23 a matsayin gudunar wa, sai kuma kudin dako watau na jigilar man fetur ya tashi a N3.89.
Akwai sauran kudi kamar na MTA da na karaso da mai da za a rika karbar kusan N8 a kan kowace litar man fetur kamar dai yadda hukumar PPPRA ta sanar.
Wannan sauya-sauye da aka samu ya na nufin cewa litar fetur zai kara kudi a gidan mai. Idan aka tara duka wadannan kudi, za a saida fetur a gidan mai a kan N212.
Tun kwanaki kun ji labari cewa danyen mai ya tashi a kasuwa, shiyasa aka fara tunanin cewa farashin litar man fetur zai iya kai wa tsakanin N185-N200 a Najeriya.
‘Yan kasuwa sun bayyana cewa a yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi, idan ba dai za a sake shigo da tsarin tallafi ba.
Daga Comr Abba Sani Pantami