Kannywood

Jerin matan Kannywood 8 da ake zargin sun yi bilicin bayan samun daukaka a harkar

Advertisment

A cikin wannan labarin za mu kawo muku sunaye, hotuna da kuma takaitaccen bayani dangane da jaruman Kannywood mata guda takwas (8) da ake zarginsu da sauya launin fatarsu bayan samun daukaka a fim.shafin labarunhausalabarunhausa na ruwaito

  1. Fati Washa

Jarumar ta dade ana damawa da ita a harkar fim din tun tana bayyana a matsayin ‘yar rawa har ta fara fitowa a tauraruwa a manyan fina-finai. Saidai an kula da yadda launin fatarta ya sauya bayan ta samu karbuwa a harkar.

fati washa
Fati Washa

2. Sadiya Kabala

Da forko ta fara bayyana a fina-finai, sai dain ta dena kasancewar ta fi mayar da hankali akan sana’arta ta siya da sutturu. amma ga wadanda su ka santa, za su kula da cewa launin fatarta ya sauya gaba daya.

Advertisment
sadiya kabala
Sadiya Kabala

3. Mansura Isah

Mansurah tsohuwar jarumar Kannywood ce kuma furodusa a halin yanzu. ita ce tsohuwar matar Sani Danja wanda ake zargin a masana’antar su ka rabu. Ita ma kwanan nan launin fatarta ya fara sauyawa.

mansura isa
Mansura Isah

4. Halima Atete

Haima ta dade tana cin zamaninta a masana’antar kasancewar ta iya hawa ko wanne matsayi aka sanya ta. Sai dai njama’a sun kula da yadda a hankali launin fatarta ya dinga sauyawa akan tsofaffin finafinanta.

halima atete
Halima Atete

5. Fati KK

Fati KK tsohuwar jarumar Kannywood ce wacce ta taka rawa sosai a fina-finan da ake yayi shekaru kusn goma da su ka gabata kamar Ban Sake ta ba, Mijina ne da sauransu. Bayan mutuiwar aurenta ne da ta dawo masana’antar da farar fata.

fati kk
Fati KK

6. Maryam AB Yola

Maryam AB Yola tsohuwar jaruma ce wacce ta fara fitowa a shirin Adam Zango mai suna Nass, wanda daga bisani jarumin ya aureta. Sai dai bayan auren nasu ya mutu ne ya dawo masana’antar da farar fata wacce har ta kai ga wasu basu gane ta ba. Ya fito a shirin Hafiz, daga bisani ta fita gabadaya daga masana’antar.

maryam ab
Maryam AB yola

7. Sadiya Haruna

Sadiya Haruna ma tsohuwar jaruma ce wacce ta samu matsaloli kwarai da wasu manya a masana’antar kamar Alhassan Kwalle, Teema Makamashi, Isah A Isah da sauransu. Ita ma launin ta ya sauya kwarai.

sadiya haruna
Sadiya Haruna

8. Umma Shehu

Umma Shehu ma tsohuwar jaruma ce, duk da dai dama tana da hasken fata amma ta kara musamman idan aka ga yadda ta sauya a cikin shirin Gidan Badamasi.

umma shehu
Umma Shehu

 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button