Aure Nayi A Thailand Shiyasa Anka Daina Ganina A Harka Fim – Jaruma Rashida Lobbo
FIM: An samu shekara ɗaya kenan ba a ganin ki a industiri ko ma a Nijeriya baki ɗaya. Sai aka riƙa ganin hotunan ki daga Bangkok, babban birnin ƙasar Thailand. Wasu sun ce aure ki ka yi a can. Ya gaskiyar maganar ta ke?
RASHIDA LOBBO: E, aure na yi a can.
FIM: Ikon Allah! Ashe auren ki ka yi. To me ya sa ki ka ɓoye maganar auren har tsawon shekara ɗaya tunda abin farin ciki ne? Ba ki so a taya ki murna ne?
RASHIDA LOBBO: Ra’ayi na ne kawai wallahi.
FIM: Ba a yi taron ɗaura aure ba kenan? Domin ba mu ga ko da hoton taron kin ɗora a shafukan ki na soshiyal midiya ba.
RASHIDA LOBBO: An yi, ban ɗora ba ne saboda ‘is my private life’.
FIM: Ya sunan mijin naki, kuma shi mutumin ina ne?
RASHIDA LOBBO: Sunan shi Abubakar, kuma ɗan Mali ne.
FIM: Wane irin aiki ya ke yi? Sannan me ya kai ku zama a Bangkok har tsawon wannan lokaci?
RASHIDA LOBBO: Aikin gwal ya ke yi kuma shi a can ya ke zama. Ya yi shekaru misalin 26 a can.