Labarai

Labari mai Ban Tausayi Al’ajabi : Talauci masifa Ne, Talauci Bala,I Ne musamman A Cikin Al,ummar Da Basu Damu Da Temakawa Talakawa Ba….

An sanar dani cewa labarin ya faru a wata jiha dake arewacin Nigeria…..

Bayan an idar da sallar magariba, kawai sai akaga wani mutum ya taso ya karbi microphones daga hannun ladanin masallacin inda yace…..

JAMA,A ZAN CANZA ADDINI….

JAMA,A WALLAHI TALLAHI ZAN KOMA ADDININ KIRISTA.. tunda dai ku baku kyakkyawar niyar temakawa mabukatan dake bukatar temako a wajenku…

Jarina ya karye ko kasuwar bana iya zuwa, dama gaba daya jarin bai wuce dubu ishirin ba, iyali na basu da abun da zasuci… wallahi yau sama da kwana uku kenan rabon da a dora girki a gidana…

Ya nuna wani mutum a masallacin yace sau biyu ina zuwa gidanka amma ko kallon arziki bakayimun bayan kana ganina kasan ina bukatar temako, kai kanka liman na sanar dakai halin da nake ciki amma ko naira goma baka bani ba, duk da cewa Allah ya horemaka abun da zaka iya tallafamin…..

Kamar wasa naje gidan Pastor Ibrahim ina sanar dashi halin da nake ciki ya bani naira dubu biyar tare da yimun alkawarin ranar lahadi zai sanar da matsalata a church, zaisa a taramun kudin temako…..

Tsakani da Allah bana son rabuwa da addinin musulunci, amma fa wallahi idan kukaki temakamun to bani da zabin daya wuce in canza addini, tunda dai Ai Allah ne da kansa yace Masu kudi a cikin musulmai su dinga temakawa marasa kudi irinmu, amma kunki……

Yau saura kwana Hudu waadin Pastor ya cika, idan har baku taimaka mun ba, zuwa lokacin idan su kiristoci sukayi, to cikinsu zan koma, daganan na samu hujjar cewa rashin temako daga yan,uwa na musulmi yasa na koma addinin kirista wadanda suka temakamun……

TALAUCI KENAN……..

Daga Rabiu Biyora

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA