Labarai

Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje

Advertisment

Gwamnatin tarayya ta ayyana neman ‘wasu mazauna gidan yarin Kuje dake Abuja da suka tsere. ‘Yan ta’adda sun kai wa gidan gyaran halin dake babban birnin tarayya farmaki a daren Talata.

Sama da masu laifi 900 ne suka cika bujensu da iska wadanda suka hada da ‘yan Boko Haram da aka garkame a gidan yarin.

A ranar Juma’a, gwamnatin tarayya ta saki sunaye da hotunan ‘yan gidan yarin da suka tsere, jaridar TheCable ta ruwaito.

Prisoners Kuje
Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje
Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje Hotuna: FG ta ayyana neman ‘yan Boko Haram 69 da suka arce daga magarkamar Kuje

‘Yan ta’addan ISWAP sun yi ikirarin cewa su ke da alhakin kai wannan mummunan harin.

Shuaib Belgore, babban sakataren ma’aikatar cikin gida, yace ‘yan ta’addan sun bayyana a shirye sosai domin kai farmakin balle gidan yarin.

“Da farko sun kasa nassarar samun shiga, amma sai suka hari wani sashi na bangon da manyan abubuwa masu fashewa wanda hakan ya ruguza bangon.

“Jami’an tsaron dake kasa sun yi duk abinda zasu iya domin dakile farmakin, amma sun zo da yawan da ba za a iya hana su aika-aikar da suka shirya ba.

“Sun dinga fada cike da kwarewa amma abun takaici sai da aka yi karantsaye kan tsaron. Karin jami’an tsaro sun bayyana lokacin da suka yi rabin aika-aikar. Daga bisani aka fatattake su. A lokacin da suka shigo, sun halaka jami’in NSCDC daya wanda yayi kokarin dakile su.

“Maus laifin su 994 ne nan. Mun gane cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne kuma sun zo ne domin kubutar da abokan ta’addancinsu.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button