Yadda Zahra Mansur ya cucemu Naira ₦206k – Cewar Audu Bulama Bukarti
Babban lauyan nan Audu Bulama Bukarti ya bada labarin yadda Musa L Maje mai amfani da sunan mace Zahra Mansur ya cuce ma’aikatrsu makudan kudi Kamar yadda Audu Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na Facebook
Ba dukkan wanda Zahra Mansur ya cuta bane manemin mata. Nima ya cuci ma’aikatarmu N206,000 kudin ticket din zuwa Uganda domin aiki. Dalili kuwa shine ya yi mana karya cewa a can ya gama karatun medicine kuma ya yi aikin duba marasa lafiya cikin kauyukan musulmin Uganda. Ni kuma ma’aikatarmu suna taimakawa kayyuka ne a Uganda da Congo amma kasancewar su Amurkawa, ba su da alaqa mai karfi da al-ummar Musulmai. Saboda haka ma fi yawan masu amfana da tallafinsu ba musulmi bane.
Da na fara da su aiki watanni biyu da suka wuce, daya daga manyan aikin da suka so na maida hankali a kai shine kulla alaqa mai karfi da Musulmai. Ni kuwa na sanar da su cewa akwai wata ‘yar Najeriya da ta yi karatu a can da za ta iya taimaka mana. Mu kayi waya da shi Zahra Mansur ofishinmu suka tura masa kudin jirgi 206k. Ni kuma na yi magana da matar wani tsohon ambasada da ke zaune a Kampala cewa idan Zahra Mansur ta zo, za ta zauna a gidansu har mu gama aikin. Daga baya mu ka gane dan damfara ne. Na so in bibiyi maganar, har ma na dan wannan rubutun na kasa a Facebook on 14 May 2022, amma ma’aikatarmu suka ce in bar maganar.
Asalin sanin sanin Zahra Mansur kuwa ya fara lokacin da na je Uganda a November 2021. Lokacin da ya ga hotunanmu da daliban can, sai ya tuntu6e ni cewa a can ya gama, kuma ya ce ya ji muna maganar cewa ana neman likitoci a Ingila a shirin Fashi Baki da muke da Barrister Abba Hikima da Jagora Jaafar Jaafar. Ya ce ya na son neman aikin likita a Ingila. Na ce zan hada shi da wani abokina da ya ke aikin likita a Ingila, amma ban samu damar hakan ba. Kuma daga nan ba mu sake magana ba sai da ofishin suka nemi in nemo hanyar kulla alaqa da musulmin Uganda da Congo.
Bayan mun gane cewa Zahra Mansur dan danfara ne, na nemi wasu hanyoyi na samu wadanda suka san musulmin Uganda da Congo. Cikin hanyoyin da na bi harda kiran ma’aikatan BBC irinsu Abdu Halilou da Muhamman Babalala suka hada ni da ‘yan Najeriya mazauna can. Kuma hakan yayi nasara. Alhamdulillah. Da na je na samu ganawa da kuma kulla alaqa mai karfi da musulmin kasashen biyu.
Allah Ya sani ban da6a managar banza ko ma ta soyyayya da wannan dan damfara ba ko wata a social media baS Magana ce ta aiki, wanda daga baya muka gane damfara ne.