Labarai

Shin da Gaske Tijjani Gandu yaba tafiya Kwankwasiyya ya koma tafiyar Gawuna?

Wannan labarin tun daga jiya jita jita ta fito tana yawo a kafaffen sada zumunta wanda abin ya baiwa mutane sosai mawakin wanda shine yayi wakar Abba Gida Gida wakar tun shekara 2019 ankayi ta amma haryanzu wakar tana buga lokacinta.

To shine yanzu nan majiyarmu ta samu sahihin labarin daga bakin mawakin inda ya wallafa gaskiya zance daga gare shi.

“Sunana tijjani gandu babban mai baiwa Gwamna Shawara akan wallafe-wallafe naji wasu CeCe kuce na jawo akan wadannan makakun mutanen marasa daraja cewa nabar tafiyar Abba gida gida zaɓaɓɓen gwamna Kano na koka tafiyar gawuna wannan abu ba haka yake ba, inaso inja hankalin yan uwana yan kwankwasiyya , mutane nan sun sani munfi so karfin soshiyal midiya da magoya baya a duk duniya.

Shiyasa suke so suyi amfani da Wannan dama su kullata sherate-sherate kamar yadda sunka fara sunriga sun dudiri guda dari biyu zasu fara.

Kada mu tsaya akan harkamu ta gwagwarmaya da addu’a subar da shirmin banza wacan waka bansan wanda yayi ta ba, bani ne nayi ta ba.

Tijjani Gandu ya kara da cewa ina nan tare da madugu tafiyar kwankwasiyya dari bisa dari 100%, kuma ina nan tare da Halastaccen zaben gwamnan jihar kano Engr Abba kabir Yusuf (abba gida gida) ae sun riga sun sani mai ƙaramin uban gida shi ka wahala ni nake da magudu ni nake da abba gida gida Wasallam alaikum. -inji tijjani gandu.

Ga bidiyon sanarwa nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button