Labarai

Matar aure ta halaka bokan da ya bata maganin kisa maimakon na mallakar mijinta

Advertisment

Wata matar aure ta halaka wani boka a Tudun Wadan Dan Kande da ke Jihar Kano bayan ta je neman taimako a wurinsa, LabarunHausa ta ruwaito.

Safiya ta garzaya wurin wani boka don neman taimako a wurinsa, ya bata maganin da zata zubawa mijinta ya kara sonta.

Sai dai bokan ya bukaci ta tafi bayan kwana biyu ta koma. Bayan ta koma ne ya bata maganin kuma ya sanar da ita yadda zata yi amfani da shi.

 

Advertisment

Bisa rahoton da AlfijirHausa ya bayyana, bayan ta yiwa mijinta amfani da maganin ya kwanta ciwo wanda daga nan ya sheka lahira.

Anan ne ta gano cewa maganin mutuwa bokan ya bata don ta sanya wa mijin kasancewar ya kamu da sonta.

Da ta koma yi masa korafi akan batun mutuwar mijinta, ya jajanta mata sannan ya tabbatar mata da cewa yana sonta kuma aurenta yake son yi.

Ya bukaci ta bashi dama ya aureta kamar yadda ta shaida, daga nan ta amince bayan kwanaki suka yi aure.

Ta barbada masa maganin da ya bata a baya, wanda ta sanyawa mijinta na baya ya mutu, daga nan ya kwanta ciwo. Bayan kwanaki kadan yace ga garinku.

Safiyya da kanta ta bayar da wannan bayanin bayan abin duniya ya dameta kamar yadda AlfijihHausa ta shaida.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button