Labarai

Wani matashi ya rasu jiya da dare a gidan kallon kwallo yayin wasan Real Madrid da Man City a Kano

Mun samu wani labari mai dimautarwa yayin da wani matashi ya rasa ransa ana tsaka da kallon kwallon wasan Real Madrid da Man City a Kano.

Kamar yadda wakilin LabarunHausa.com ya bayyana, lamarin ya faru ne a wani gidan kallo da ke Airport Road wanda ke kallon gidan man Total da ke Brigade a Kano.

A ranar Laraba da dare an yi wasan kwallo tsakanin kungiyoyi biyu, Real Madrid da Man City wanda ya yi matukar daukar hankalin matasa musamamn masu son wasannin kwallo.

Wasan wanda ya kai har karfe 11 saura na dare ya tashi ne yayin da wasu su ke kunci, wasu kuma su ka dinga farin ciki don Real Madrid ta ci Man City.

Sai dai babu wanda zai iya bayyana musababbin mutuwar matashin don babu wanda ya lura da cewa ya rasu har sai da kowa ya watse ana tunanin bacci ne ya dauke shi.

Wani matashi wanda ya bukaci a sakaya sunansa, wanda shi ma ya yi kallon kwallo a gidan ya bayyana wa LabarunHausa.com cewa:

Jiya an tashi daga kallon ball, na fito kowa yana fitowa da misalin karfe sha daya saura kwata. Mun bar shi yana kwance, har da zan tashe shi, sai wani ya ce in bar shi tunda na ga mutane sai wucewa su ke yi babu wanda ya taba shi sai nima na wuce.

“Sai da safen nan na ji labarin wani ya rasu a silma. Sai na ce ba dai wannan mutumin da ya ke kwance a silima mai kaya masu ruwan kwai ba. Sai aka ce min ai ko a lokacin ya zama gawa.

“A gidan kallon kwallo na Queen Cinema lamarin ya faru. Ban san ko damuwar faduwar bangarensu ba ne ya kashe shi ko kuma lokaci ne ya yi ba.

“Ba a fitar da shi daga gidan kallon kwallon ba sai yau da safe saboda kowa ya watse ya bar shi a wurin.”

Muna fatan Ubangiji ya gafarta masa ya kuma sa ya huta. Ameen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button