Audu Bulama ya yi kaca-kaca da Dan jahannama yayin muhawara ta bidiyo
Alhamdulillahi Barrister audu bulama bukarti ya tattauna da wani matashin yaro wanda yake kiran kansa danhajannama wanda tattaunawar tayi matukar tasiri sosai.
Barrister audu bulama bukarti yace sunyi akan maudu’i shidda wanda shi danhajannama yake ikirarin cewa babu a doron duniya.
Wanann tattaunawa itace ta farko da shi audu bulama bukarti da shi yaron maudu’i na Farko shine kana Danjahannama yana kore cewa Annabi adam ba shine mutum na farko da asalin mutane a doron duniya ba.
Shi danhajannama yace miyasa idan akwai mutum na farko kuma ance Annabi adam idan fari ne yakamata kowa ya zama fari, idan kuma baki ne ya kamata kowa ya zamo fari
Alhamdulillahi Barrister audu bulama bukarti yayi cikakken bayyani akan nau’in sanadarin da ke cikin dan adam wanda shine yake girma domin fatar mutum ta zamo baka ko rashin samun shi isashe fata ta zamo fara a binciken fasaha da kimiya tabbas ya kowa hujjoji sosai wanda har shi wanda ke kiran kansa danhajannama ya yarda da hujjojinsa.
Ga bidiyo nan Barrister yayi bayyani dalla dalla.
Wannan shine Bidiyo na farko a turanci ana kiransa “Part 1” akwai saura ku kasance da hausaloaded a koda yaushe zamu kawo muka sauran muhawara da sunkayi.