Labarai

Yan Najeriya Miliyan 95 Za Su Fada Kangin Talauci A 2022 — Bankin Duniya

Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto inda ya yi harsashen cewa yawan talakawa a Najeriya zai karu zuwa mutum miliyan 95 nan da karshen 2022.Aminiya na ruwaito

Wannan na dauke ne cikin wani rahoto da ya fitar don samar wa Najeriya makoma ta gari.

Ya ce rage radadin fatara ya samu koma baya tun a 2015, inda ’yan Najeriya da dama suka fada cikin kangin talauci na tsawon shekaru.

A cewar bankin, an yi harsashen adadin mutanen da za su fada cikin kuncin rayuwa a Najeriya zai kai miliyan 9.4 a karshen 2022.

Kazalika, ya ce rahoton wani kokari ne na neman hanyoyin fitar da ’yan Najeriya daga kangin rayuwa.

Wata kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa yawan talakawan Najeriya ya kai kashi 42.8 cikin 100 a 2020, wanda yana kasa da kididdiga ta 2010 da kuma ta 2011 da ya kai kashi 43.5 cikin 100.

Har wa yau, bankin ya ce akwai yiwuwar wadanda za su fada talauci ya haura idan aka yi la’akari da yadda yawan al’ummar Najeriya ke karuwa a kodayaushe.

Alkaluman da aka zayanna a baya-bayan nan sun ba da kiyasin cewa talauci ya fara raguwa a farkon 2010 sannan kuma ya sake ninkawa a 2015.

Sai dai wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da koma bayan tattalin arziki a 2016 sakamakon faduwar farashin mai a kasuwanin duniya.

Kazalika, rahoton ya ce bullar annobar COVID-19 ta daidaita tare da jefa sama da mutum miliyan biyar a Najeriya cikin kangin talauci.

Tuni kayan masarufi suka ninka kudinsu wajen sau hudu a Najeriya, lamarin da ya sanya masu karamin karfi shiga halin ni-’ya-su.

Lamarin ya kuma tagayyara rayuwar miliyoyin mutane, wasu da dama abin da za su ci na neman gagararsu, wanda hakan ya tilasta wasu shiga yin bara a manyan tituna da kuma lungu da sako na unguwanni.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button