Labarai

Allah ya Rabamu da Talauci: Wani Babban Basarake zaiyi Wuff da Mata ta 6 A Yau

Idan kana da rai ko wane irin labari ji kake a wannan duniya shi kuma ga wani basarake nan yana shirin yin wuff da mata ta shidda a cikin jerin matansa kamar yadda jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, zai angwance da mata ​​ta shida, Temitope Adesegun, a gobe Litinin, 24 ga Oktoba, 2022.

Jaridar Punch ta rawaito cewa sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun Ooni, Moses Olafare, a cikin wani sakon Facebook da ga wallafa a yau Lahadi.

A ranar Alhamis, 20 ga Oktoba, 2022 me dai Sarkin ya auri matarsa ​​ta biyar kuma wa ce ta kafa dandalin Makon Kwalliya na Afirka, Ronke Ademiluyi wacce ita ce jikanyar Ooni na Ife na 48, Ajagun Ademiluyi.

A cewar Olafare, matar Ooni ta shida mai jiran gado, Adesegun, gimbiya ce wacce ta fito daga yankin Ijebu.

A cikin sakon Facebook, Olafare ya rubuta, “Olori Temitope Adesegun Ogunwusi an Ijebu Princess cum Ile-Ife Queen.

Bayan aurensa da Naomi Silekunola a watan Disamba 2021, sarkin ya auri mata biyar cikin kasa da watanni biyu.

Matan nasa su ne; Mariam Anako, wanda yanzu ita ce matarsa, Satumba 6, 2022; Elizabeth Akinmudai; Tobiloba Philips, Oktoba 9, 2022, Ashley Adegoke, Oktoba 14, 2022 da Ronke Ademiluyi, Oktoba 20, 2022.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button