Labarai

Gwamna Zulum Ya Roki Buhari Ya Bari Sojojin Chadi zuwa Nigeria domin Yaki da Boko Haram

Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya roki Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka ya gayyato sojojin Kasar Chadi su shigo Nigeria su yaki Boko Haram
Gwamna Zulum ya isar da wannan roko ne a yau Laraba lokacin da shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria gwamnan jihar Ekiti Dr John Kayode Fayemi ya kai masa ziyara birnin Maiduguri domin ya masa jaje akan harin kwanton bauna da Boko Haram suka yiwa tawagarsa a hanyar Baga
Gwamnan ya bayyana cewa yayi wannan roko ne ba don ya nuna gazawar sojojin Nigeria ba, yanaso gwamnatin Nigeria ta gayyato sojojin Mali su taimakawa sojojin Nigeria murkushe Boko Haram
Kamar yadda Datti Assalafy ya wallafa ,gwamna Zulum ya kara da cewa, a tarihi babu inda rundinar sojiji na wata kasa daya tilo da ta taba yin nasara akan yaki da ta’addanci, sai an samu hadin kai da taimako daga wata rundina ake haduwa aci nasaran yaki da ta’addanci
Allahu Akbar! ba shakka Gwamna Zulum ya fadi tsantsar gaskiya, ga misali nan da Kasar Amurka kasar da ake cewa tafi kowace kasa a duniya karfin tsaro da tattalin arziki, amma duk yakukuwan da Amurka tayi a gabas ta tsakiya sai da ta gayyato sojojin haya ta dauki nauyinsu kafin ta kai ga nasara
Na san wannan roko da gwamnan Zulum yayi ba zata yiwa manyan maciya amanar tsaron Nigeria dadi ba, zasu kara jin haushinsa da kuma tsanarsa, watakila ma su nemi rayuwarsa kamar yadda suka saba, saboda suna ganin zai toshe musu hanyar neman kudi da sunan yaki da Boko Haram
A yanzu Boko Haram/ISWAP sune suke wahalar da Nigeria a yakin da akeyi, suna yankin sahara, sojojin Nigeria yakin sunkuru (Bush Operation) suka iya suka kware, ba su kware a yakin sahara (Desert Operation) ba sam, sai da fitinar Boko Haram tazo kafin suka fara
Sannan sojojin Nigeria basu da motoci da kayan yakin sahara, sojojin Kasar Chadi su ke da wannan, sunfi kowace kasa a duniya kwarewa a yakin sahara, kuma sun jima suna gumurzu da ‘yan tawaye tun kafin Muhammad Yusuf yayi wayo ya taso ya kafa Boko Haram, ba shakka sunfi sojojin Nigeria sanin dabaru da sirrin yakin ‘yan tawaye da na ta’addanci, ni akwai kwamandan yakin Boko Haram da ya yabbatar min da haka a inda maciya amanar tsaron Nigeria suka boyeni tare da mayakan Boko Haram da aka kama a Abuja, ya fada min cewa sunfi tsoron sojojin Chadi akan na Nigeria
Shugaba Buhari ya zama wajibi a gareka ka amsa rokon Gwamna Zulum ka gayyato sojojin Kasar Chadi, domin shine hanya kadai na kawar da Boko Haram daga yankin sahara tafkin Chadi, hakan ba abin kunya bane, kuma ba gazawa bane, idan baka gayyato su ba to ka sani cewa tarihi zai ajiye wannan batun, kuma za’a zargeka kamar yadda aka zargi magabancinka Jonathan da kin daukar matakin da ya dace
Zamu zuba ido mu gani, Baba Buhari zai yadda da shawaran Gwamna Zulum ko zai karbi shawaran maciya amanar da ba sa so a gama da Boko Haram saboda kudin da suke samu
Allah Ka nuna mana karshen Boko Haram
Allah Ka kare mana Gwamna Zulum Amin Yaa Hayyu Yaa QayyumMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button