OVER Protocol Airdrop : Hanyoyin da mutane zasu samu Over Protocol Airdrop da kuma ka’idojinsu
🌐 Points: Mutanen da suka tara points a Over wallet ta hanyar amsa tambayoyi kullum, za’a juya musu wannan points din zuwa $OVER coin. Ka’idar samun airdrop ga wayanda suka tara points shine suyi sybil detection, wato KYC. Flipster da Hashkey Global sune exchanges din da Over Protocol suka bada dama ayi KYC dasu a baya, wayanda basuyi ba kuma Over Protocol sun kawo form jiya domin su chike. Wannan chike form din zai tashi amatsayin KYC dinsu. Har zuwa yanzu basu fadi conversion rate na points zuwa $OVER coin ba. Ma’ana basu fadi duk $OVER coin daya daidai points nawa yake ba.
🌐 Cards: Cards shine referrals da mutum ya tara. Dole sai referrals dinka sunyi sybil detection test (KYC), kafin ka samu rewards dinsu. Duk wanda baiyi KYC ba, bazaka samu rewards dinsa ba.
🌐 Open Beta Testnet One (OBT1): OBT1 shine wanda mukayi shi a computers amatsayin nodes na Over Protocol domin muyi testing blockchain dinmu. Babu wata ka’ida akan wannan domin samun airdrop. Ma’ana duk wanda yayi OBT1 automatically zai samu airdrop. Duk Over wallet din da tayi OBT1, zata samu airdrop dinta na points dana OBT1 da tayi koda batayi sybil detection ba (KYC). Yin OBT1 tamkar yin KYC ne, kamar yanda suka sanar lokachin da za’a fara OBT1. Har zuwa yanzu basu fadi rewards na wayanda sukayi OBT1 ba.
🌐 Open Beta Testnet Two (OBT2): Bayanin OBT1 da nayi a sama, shine dai akan OBT2. Saidai Over wallet din data tara points, tayi OBT1 da OBT2, sai tafi Over wallet din data tara points sannan tayi iya OBT1 kadai samun rewards, wato $OVER coin.
🌐 OKX Cryptopedia: Wayanda suka dinga claiming daily Over testnet tokens achikin OKX suma airdrop dinsu daban. Yawan airdrop na OKX Cryptopedia zai banbanta gwargwadon adadin kwanakin da mutum yayi claiming, da kuma transactions da yayi dashi ta hanyar turashi zuwa wasu OKX wallet ko Over wallet da yayi.
🌐 Nethers NFT: NFT ne da Over Protocol suka sayar dashi. Over Protocol sun sanar cewa duk wayanda suka sayi Nethers NFT za’a basu damar juya duk NFT daya zuwa 764.64 $OVER coin a ranar 30th August.
Rubutawa : sunusi Danjuma Airdrop