Labarai

‘2023, ka yi kowa ban da Osinbajo – Dr Musab Isah Marafa

Jiya na yi gajeren post mai cewa ‘2023, ka yi kowa ban da Osinbajo.’ Mutane da yawa sun buƙaci in yi sharhi a kan magana ta, in faɗi dalilai na. Farko ina ba hanƙuri rashin yin sharhi tun jiya saboda lamarin aiki da guje-guje na yau-da-kullun. Wato akwai dalilai guda biyu da ya sa ni ke ganin bai kamata a yi Osibanjo ba. Na farko ya ta’allaƙa ga addini, na biyu kuma mahanga ce ta siyasa.
Ga mahanga ta addini, ba wai ka da a yi Osinbajo saboda ya na kirista ba, a’a. Hasali ma ni ba ni akan fahimtar cewa in Musulmi da Kirista sun tsaya takara to haramun ne (ko ma kafirci in ji wasu) ka zaɓi kirista ka bar Musulmi. A ƙasa irin Najeriya da a ke cakuɗe da Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, ƙasar da ta ke kan tafarkin dimokraɗiyya, mutum ya na da damar ya goyi bayan wanda ya ke ba Musulmi, ko da su na takara da Musulmi, in ya na ganin shi wanda ba Musulmin ba zai fi ba da shugabanci nagari a mahanga ta gama-gari kuma shi ne zai tamake ka ka cimma na ka burika a mahanga ta na ka muradu na rayuwa.
Amma tabbas shi Osibanjo ba wai ko wane irin kirista ba ne. Limamin coci ne wanda ke ganin cewa aikin shi ne ya tabbatar da da’awar kiristanci a duk in da ya ke ta hanyar ba da fifiko ga kiristoci ƴan-uwan shi kuma musamman waɗanda su ka fito daga cocin shi ta RCCG, da kuma ba da fifiko ga addinin shi a duk in da ya samu kan shi. Mutum ne wanda zai tabbatar da cewa Musulmin kudu-ma-so-yammancin Najeriya sun ƙara rasa ko wane irin tasiri a zamantakewa da siyasar wannan yanki na su kamar yadda ya ke yi a duk wani mataki da ya samu a tsawon rayuwar shi ta aiki.
Duk da cewa rubutun Prof. Kperogi ya yi tasiri ga post ɗin da na yi jiya, amma na ɗauki lokaci ina tattauna maganar Osinbajo da jama’a daban-daban cikin su kuma akwai Yarbawa Musulmi da mu ke zaune tare da su a nan Saudiya. Sannan na daɗe da yanke hukuncin cewa wannan mutumen zai yi ma Musulunci illa sosai in ya samu muƙami na Shugaban ƙasa saboda halaye da yawa da ya ke nunawa tun kafin ya kai ga madafun iko. Tabbas Prof. Kperogi ya kawo hujjoji masu nuna cewa Osinbajo zai iya kawo babbar illa ga ƙasa a ƙoƙarin shi na ƙarfafa addinin kiristanci ta ko wane irin hali.

'2023, ka yi kowa ban da Osinbajo - Dr Musab Isah Marafa
Dr Musab Isah Marafa

Wani za ice, to ai abun da a ke dubawa shi ne shin zai yi aiki ga ƙasa ko ba zai yi ba? Sannan su Musulmi da su ka yi ta riƙa muƙamai mi su ka yi mu na? Amsa ta ita ce, tabbas mu na son wanda zai yi aiki ga ƙasa kuma ko da ba Musulmi ba ne ya kamata a goya mai baya, to amma ba irin Osinbajo ba. Ni ba zan iya zaɓen – kuma zan gargaɗi mutane game da zaɓen – wanda ayukkan shi za su iya yin zagon-ƙasa ga cigaban addini ko da a ƙasashen Yarbawa ne kawai balle ma illar za ta kai ko ina a cikin ƙasa.
Abu na biyu kuma shi ne ga mahanga ta siyasa. Tun da PMB ya samu mulkin Najeriya daga 2015 zuwa yanzu babu abun da mu ke gani in ba tasku ba. Rayuwa ta yi tsananin da ba ta taɓa yi a tarihin Nigeria ba. To ta yaya za mu ɗauki ƙuri’un mu mu ba Mataimakin shugaban ƙasan da da shi a ka yi shekara 8 a na wanga mulki na rashin adalci da rashin iya gudanarwa. Mataimakin da shi ne shugaban majalisar tattalin arziki ta ƙasa, shi ke da alhakin tsaren-tsaren tattalin arziki wanda kowa ya san irin bala’in matsin da tsare-tsaren gwamnatin su su ka jefa ƙasa ciki.
Irin wannan dalilin shi ya sa ko a shekara ta 2019 na yi ta kira da ka da mu sake zaɓen PMB. Rashin taskai ne a ce mutumen da ya yi sanadin jefa ka cikin uƙuba kuma a ce mu sake ba shi dama ya tsunduma mu cikin wani bala’in na daban. Da Osinbajo da Buhari duka jirgi guda ya ɗauko su. Sun gama ragargaza ƙasa, alal aƙalla su koma gida su zauna ba a sake saaka ma Osinbajo da mulkin Najeriya ba.
Cewa ‘2023, ka yi kowa ban da Osinbajo’ ya na nufin shi ne mafi rashin-cancanta cikin waɗanda su ka nuna aniyar su ta shiga zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa amma tabbas ka tantance kafin ka nuna goyon bayan ka ga ɗaya daga cikin masu nema ko daga wace jam’iyya ya fito. Babbar matsalar a halin yanzu duka masu neman su na da wani laaɓo wanda za ka ce ya kamata a nisance su. Duk da mutane sun ɗebe tsammanin samun shugaba na gari ganin irin kasawar Buhari bayan mun kyautata ma sa zato, duk da haka ka san cewa da baƙi-ƙirin gara baƙi-baƙi.
Ka kalli masu neman shugabanci da wakilci a ko wane mataki na zaɓe, ka yi iyakar nazarin ka, ka zaɓi wanda ka ke gani mai yiyuwa zai iya canza al’amurra ko ya ba da wakilci nagari. Kai ba laifi ba ne ma ka zaɓi wanda ka ke ganin zai taimaka ka cimma muradun ka na rayuwa ko na addinin ka. Amma ka da ka zauna ka ce duka ba na ƙwarai ba ne don haka ba za ka yi zaɓe ba. In ba ka yi ba, wasu za su yi, kuma a haka za ka haƙura da zaɓen na su. Sannan ka bi da addu’ar Allah Ya zaɓa mu na mafi alherin shugabanni ga lamurran duniyar mu da ayukkan lahirar mu ko da ba waɗanda mu ke so ba ne.”
Dr. Musab Isah Mafara

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button