Mai Mala Buni Muka Sani, Babu Ruwanmu Da Wani Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Cewar Hukumar INEC
Hukumar zabe ta kasa INEC ta yi watsi da wasikar gayyata zuwa taron majalisar zartaswa na gaggawa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda bata ga sanya hannun Gwamna Yobe, Mai Mala Buni, da na Sakatare AkpanUduohehe ba.
Da yiwuwan yunkurin cire Mai Mala Buni karfi da yaji ya fuskanci babban matsala.
INEC, a wasikar da ta aike ranar 9 ga Maris, 2022 kuma Sakatarenta, Rose Oriaran Anthony, ta rattafa hannu, hukumar ta ce APC ta saba ka’idar Article 1.1.3 na dokokin ayyukan jam’iyyun siyasa.
INEC ta kara da cewa bisa sashe na 82(1) na dokar zabe, akwai bukatar a sanar da ita ana saura kwanaki 21 akalla kafin wani babban taro, ko ganawa don maja da zaben sabbin shugabanninta.
INEC ta bayyanawa APC cewa saboda haka tayi watsi da wasikar.
Daga Comr Abba Sani Pantami