Labarai

Farashin litar man jirgin sama ta tashi daga N190 zuwa N670 a makonni 2

Kamfanonin jiragen sama a Nijeriya sun koka cewa farashin man jirgin sama ya yi tashin gwauron zabi da ga N190 zuwa N670 a kowacce lita ɗaya a cikin makonni biyu.
Kamfanonin sun kuma yi zargin karkatar da man zuwa kasuwar bayan-fage da wasu masu kawo man jirgin sama samfurin Jet A1 ke yi, wanda hakan ya sa farashin ya tashi ya kuma haifar da karancin sa.

Kazalika kamfanonin sun nuna damuwarsu kan yiwuwar karyewar kamfanonin jiragen sama a Najeriya, inda su ka kara da cewa sun damu matuka dangane da ci gaba da ƙarin farashin man jiragen.
Masu kamfanonin sun bayyana haka ne a yayin zaman kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken karancin man jiragen sama..

Allen Onyema, Shugaban Kamfanin Air Peace, ya ce a cikin makonni biyu farashin man jiragen ya tashi daga Naira 190 kan kowace lita zuwa Naira 670..

Daily Nigerian hausa ta ruwaito Onyema ya ce ba don kakar siyasa ta zo ba, da kuma ganin cewa wannan gwamnatin na tallafa wa ɓangaren sufurin jirgin sama, da tuni masu kamfanonin sun rufe kamfanonin US a ƙasar.
Ya ce ma’aikatan ba za su iya kai wa sa’o’i 72 masu zuwa ba a cikin wannan hali ba sabo da ɗumbin bashin da ke kan su, inda su ke fargabar kada hukumar kula da kadarorin Najeriya, AMCON ta rurrufe ofisoshin su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button