Labarai

Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

Advertisment

Kaduna – Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fahimci yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba. Tambuwal a ranar Asabar, 19 ga watan Maris, ya ce alakar da ke tsakanin shugaban kasar da Najeriya tamkar ‘auren dole’ ne, jaridar legit  ta rahoto.
Da yake magana a sakatariyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kaduna, gwamnan na jihar Sokoto ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da lalata kasar, Thisday ta rahoto.
 
Tambuwal ya ce:
Mun ga cewa APC ba ta iya ba kuma ba za ta iya kula da harkokinsu a matsayin jam’iyya ba. Ta yaya za ta iya samar da mulki da shugabancin kasa mai girma da wuyan sha’ani kamar Najeriya? Mun san rikicin APC a yau.
“Na fadi wannan a wani wajan kuma zan maimaita, lamarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace.
“Da wuya a samu fahimta ko zaman lafiya. Shugaban kasar bai fahimci Najeriya da yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.” 
 
Tambuwal ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ya fahimci kasar kuma wanda zai iya samar da daidaito kan muhimman al’amuran da suka shafi kasa.
Domin ganin mun magance matsalolin Najeriya a yau, akwai bukatar mu samu babban jagoran kasar nan mutumin da ya fahimci Najeriya da kanta. Wadanda ke da abokai a duk wani lungu da sako na kasar nan.
Za su iya tuntuba sannan su dauki hukuncin bai daya kan lamuran da suka shafi mutanen kasar nan. Za ka iya aikata hakan ne kawai idan kana da hanyar sadarwar da ake bukata. 
“Muna bukatar mutum da zai iya hada kan kasar nan. Mutum da ya ke tsantsar dan Najeriya. Wanda ya fahimci yanayin shugabanci na zamani.” 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button