Labarai

Tsohon Shugaban NNPC Maikanti Baru Ya Rasu

Advertisment
Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya, NNPC Maikanti Kacalla Baru ya rasu.
Wata majiya daga iyalinsa ta tabbatar wa BBC rasuwar tsohon shugaban na NNPC.
Shi ma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya tabbatar da rasuwar mutumin da ya gada, a wani sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Tsallake Twitter wallafa daga @MKKyari

Karshen Twitter wallafa daga @MKKyari
Kyari ya ce: “Dan uwana, abokina kuma gwanina, Dr Maikanti Kachalla Baru, tsohon shugaban NNPC ya rasu a daren jiya. Mutum ne abin koyi. Allah Ya yafe kura kuransa sannan ya yi rahama a gare shi”.
An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya a 1959 kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.
Ya soma aiki a babban kamfanin man na Najeriya a 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban na NNPC.

maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin
shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

Shi ne shugaban NNPC na goma sha takwas.
Ya bar mata biyu da ‘ya’ya da dama.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button