Alkawali ya cika Nazir Sarkin waka ya tura Naira Miliyan 1M na Fati slow
A jiya ne sarkin waka nazir m ahmad yayi bidiyo inda yake cewa yayi alkawalin zai baiwa fati slow naira miliyan daya akan irin bidiyon da tayi akan kalaman ladin cima mama tambaya inda har Nazir m ahmad sarkin wakan tsohon sarkin kano ya fito ya gasgata maganarta da su Ali nuhu na karyata.
Wanda har mutane suke ganin kamar ba gaskiya bane bazai iya basu kudin ba.
Majiyarmu hausaloaded ta samu daga majiya mai karfi shafin mansurah isah ta bayyana cewa tabbas har sarkin waka ya tura kudin fati slow a cikin asusun today life foundation. Inda ta wallafa a shafinta ga abinda take cewa.
“Assalamu alaikum. Malam @naziru_sarkinwakar_san_kano ya aiko da Naira Miliyan daya cikin account din @todays_life_foundation domin mu taimakawa Fatima ( Fati slow ) juyawa.
Yace ya yarda da Mindset dinmu kuma ya yarda zamuyi Mata abinda ya dace.
Fatima Tana godiya Kwarai dagaske.”
View this post on Instagram
A jiya daine jaruma fati slow ta samu ganawa da sarkin waka nazir m ahmad kamar yadda majiya ta tabbata.
View this post on Instagram