Bidiyon Fati Slow yayin da take ba Naziru sarkin waka hakuri da godiyar Kyautar Naira miliyan 1 da ya bata
Legit sun ruwaito cewa harma jarumar ta kalubalance shi da ya rantse cewa shima baya aikata hakan.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafin nata, Fati ta ce dama chan talauci ne ke damunta amma ta nutsu yanzu.
Ta kuma tabbatar da cewar mawakin ya bata naira miliyan dayan da ya yi mata alkawari inda ta nemi yafiyarsa a kan cin mutuncin da tayi masa.
An jiyo Fati na cewa:
“Ga ni ga sarkin waka Naziru, nagode Allah ya saka da alkhairi, ya bani naira miliyan daya. Dama harkac e ta kebura (talauci) kuma babu wanda bai san ta ba. Na nutsu yanzu. Komai ya wuce sarki ka yi hakuri, Wallahi na yi maka hau, kuma ka ce ka yafe mun Alhamdulillahi wallahi nagode ma Allah, wannan ma arziki ce a rayuwa ta duniya.”
View this post on Instagram