Kannywood

Wata sabuwa ! Zargin bin bokaye bin maza da sata a matan kannywood

Da in zagi Annabi gar a dau rain inji yar Tiktok

Wata sabuwa ! Zargin bin bokaye bin maza da sata a matan kannywoodSababbin jarumai masu tasowa a masana’antar kannywood masu tasowa da wasu ke musu lakabi da jaruman YouTube ko jaruman series sun yiwa wata kawar su tofin alatsine a dandalin tiktok inda suka yi layi daya bayan daya suna la’antar ta da fadin aibunta da suka hada da bokaye da asirce asircen bin maza daraktoci da kura da kare da doki banda zargin warin jiki da baki da sauransu da zargin sata sukayi ga jarumar.

Sai dai duk wannan rubdugun zagi da cin zarafinta sukayi mata basu kama sunan ta ba a cewar su ta san kanta sai dai wannan zagi da suka yi ga kawar su ya bar baya da kura domin kuwa wasu na kallon abun da tamkar kansu suke tonawa asiri suka kara fadar abin dama ake zargin wasu suna yi ne a masana’antar.

Binciken mu ya tabbatar muna da wacce suke zagin daga wata majiya mai tushe inda ya bayyana ita ma yar masana’antar ce kuma kawar su duka suna tare mafin ta hado su da ita suyi mata wannan tijara.

Ga bidiyon nan a kalla…….

A wani labarin kuma wata budurwa ce da tayiwa malamai kudin goro kan wata lakcha da Sheikh abdallah yayi akan bincike kafin aure inda wani malami yayi fassara maganganun ta da cewa har Annabi s.a.w zai iya shiga ciki duk yana cikin wannan bidiyon.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button