Kannywood

Amdaz ‘Excellency’ ya angwace, tare da godiya ga al’umma baki daya

Advertisment

Fitaccen jarumin kuma mawaki Abdallah Amdaz “Excellency” ya angwace jiya aka daura aurensa da amaryasa a garin Maiduguri da ke jihar Borno da ke arewacin Nijeriya.

Abdallah Amdaz yayi murna matuka ga ilahirin masoyansa wanda sunka samu halarta daurin aurensa da wadanda suka taya shi da addu’a.

Amdaz ya wallafa sakon godiya da bangajiya ga maza da mata da sunka samu hallarta daurin aurensa wanda yake yiwa kowa fatan alkhairi.

“Alhamdulillah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda yasa akayi taron bikina lafiya, cikin Kwanciyar hankali da yalwar arziki, Allah ya sakawa duk wanda suka halarci tarukan da mukayi da alkairi, wanda suka aika mana da sakon fatan alkairi suma muna godiya Allah yabar zumunci.

Advertisment

Haka nan ina godiya ga duk wanda suka bani lokaci da gudunmawarsu ta kowacce irin siga Allah ya saka da alkairi.”

A madadin CEO hausaloaded suna taya mawaki kuma jarumi amdaz Excellency murna Allah ya bada zama lafiya ya bada zuri’a dayyina amin.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button