Labarai

Za a bude layukan wayoyin salula a Zamfara

Advertisment

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ce nan da ranar Talata za a bude layukan wayar salula a fadin jihar.
Ya bayyana haka ne a wurin zaben shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ranar Asabar.
A farkon watan Satuba ne aka katse layukan a wani mataki na dakile hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Bbchausa ta ruwaito Sai dai a kwanakin baya an bude layukan wayar salula da intanet da aka katse a Gusau, babban birnin jihar.
Matawalle ya kara da cewa za a sake bude kasuwannin da aka rufe sakamakon matsalar tsaro.
“Bayanan da muka samu sun nuna cewa an samu raguwar matsalolin tsaro a yankunan jihar nan, kuma nan da Litinin ko Talata za mu sake bude layukan wayoyin salula, kowa da kowa zai samu damar yin waya,” in ji gwamnan

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button