Ba na rokon kowa ya zabe ni a matsayin mataimakin shugaban kasa – Gwamna Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Asabar din da ta gabata, ya fito ya bayyana ra’ayin sa akan cewar ba ya rokon duk wadanda suka fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da su zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Zai iya samun mukamin mataimaki ga duk wanda ya fito takarar Shugaban kasa
Sunan Zulum ya fito cikin jerin sunan wanda zai tsaya a matsayin mataimakin shugaban Kasa ga duk dan takarar shugaban kasa da ya fito a jam’iyyar APC.
Zulum ya bayyana ra’ayin nasa ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, wanda ya kai ziyara jihar Borno domin ganawa da wakilan jam’iyyar APC na jihar saboda zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda zai gudana 29 ga watan Mayu.
Gwamna Zulum, wanda ya yaba wa Mista Amaechi, ya ce shi ra’ayinsa ba ya goyon bayan duk wani mai son tsayawa takara saboda ya yi imanin cewa Allah ne ke bayarwa kuma Shi yake hana mulki.


Duk wanda ya zama shugaban kasa yana tare da shi
Ya ce a matsayinsa na jagora a jihar Borno, zai yi aiki da duk wanda Ubangiji ya bawa nasarar zama shugaban kasar Najeriya.
“A gare ni mulki na Allah ne Shi ke da dukkan iko, ‘yan takara da dama sun kawo mana ziyara kuma da yawan su suna kan hanyar zuwa amma addu’ata da fatana ita ce a kullum Najeriya ta samu sabon shugaban kasa. Ba zan iya ambaton sunan wani takamaiman dan takara ba dan bani da gwani.”
Najeriya ta kasance koma baya
Ya ce Najeriya ta na fama da rashin ci gaba sosai.
“saboda shugabannin mu sun yi watsi da mutane.