Kannywood

Wata Sabuwa! Adam A Zango Ba Ummi Rahab ce Ta Farkon Yiwa……. Inji Ali Atwork

Mun wayi gari da wani labari wanda ali artwork madagwal yayi a shafin na sada zumunta na Facebook inda ya wallafa wani bidiyo da cewa dan uwan ummi rahab ne wanda duk bayyaninsa na cikin wannan sakon bayan haka kuma shi ali art work ya bayyana cewa wannan abun ba shine na farko da adam a zango yake yiwa yan mata ba.
Ga abinda ya wallafa nan domin karanta daga gareshi.

“Inna lillahi wa inna ilaihiraju’un To Jama’a Kun dai ji Gaskiyar Magana Daga Makin Dan Uwan Ummi Rahab wato Yasir Rahab Allah ya kyauta dama Musulunci yace duk abunda zakai kayi bincike karkai saurin yankewa ban gare daya hukunci shi yasa mukace jama’a kuyi bincike akan wannan lamari itafa gaskiya guda dayace daga kinta sai bata Allah ka dauwwamar damu akan tafarkin Gaskiya Allah Sarki Ummi Rahab Anso A Miki Shigo Shigo ba zurfi Amma Allah ya tsareki shine ake son a fake da kinyiBUTULCI ko kuma ba kya jin magana to jama’a ina son ku sani wannan mutumin ba akan wannan Yarinyar ya fara irin wannan Yaudarar Ba.

Yayiwa Mata da dama haka dan haka in baza ku manta ba wannan mutumin yayi rigima da mata da dama a wannan masana’anta daga karshe sai yace sun masa BUTULCI.

Saboda kawai ya nema bai samu ba daga karshe sai yayi amfani da makafin Masoyansa ta karfin Tsiya sai sun dawo mai da yarinya gurinsa dan kawai ya cutar musu da “Yar Marainiyar Allah dan ya cinmma wata mummunar manufarsa ku kuma masoyansa baku san meke faruwa ba sai kuyi ta Goya masa baya yana jin dadi yanzu kai da kanwarka ko “Yar uwarka akawa haka zaka ji dadi kawai a zo social media bata san hawa ba bata san sauka ba ace tayi BUTULCI a sa mutane suyi ta zaginta da la’anta bata jiba bata gani ba.

Wata Sabuwa! Adam A Zango Ba Ummi Rahab ce Ta Farkon Yiwa....... Inji Ali Atwork
Wata Sabuwa! Adam A Zango Ba Ummi Rahab ce Ta Farkon Yiwa……. Inji Ali Atwork
Hoto :Instagram
Daga :ali artwork, adam zango, ummi Rahab

“Yar Karamar yarinya da bata san komai ba wai ace ta bijire hakan na nufin ta tafi karuwanci kenan al’hali kuma yarinya babu inda take zuwa daga gida sai gun aikinta wannan ba dai dai bane a bata sunan “yar da duk mai sonta ya aureta shikenan zai fara mata kallon tana zuwa yawan bariki. Kace zaka Aureta ka gudu kaki komawa wanda suke sonta tsakani da Allah ka sa musu shakku akanta shi kenan kana son ka hanata Aure koh?.

Karamar yarinya a sa mutane su tsaneta babu gaira babu dalili ya kamata Yan uwa Muji tsoron Allah muguji yada jita jita Allah ma ya hana haka kuma insha Allah wannan yarinya zamu ci gaba da mata addu’a kuma insha Allah daga wannan Yarinyar Baiwar Allah insha Allah bazai kara yiwa wata “Ya mace haka ba don haka muna kara Addu’ar Allah ya kara tsare miki mutuncinki Ummi Rahab Allah ya kara baki kariya muna rokon Allah ya baki miji Nagari kiyi Aurenki ki Zauna Lafiya.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button