Kannywood

Albishirinku Masu Kallon Shirin Izzar so Nesa Tazo kusa

Albishirinku masu kallon shirin izzar so wanda manya manyan jaruman masana’antar kannywood ke gabatarwa duk sati wanda shirin mai dogon zango ne, wanda yanzu haka ana cikin kashi na 49.

Instagram : Lawal Ahmad

Shirin izzar so wanda ya samu zaratan manyan kannywood sun hada da ali nuhu,lawal ahmed aisha najamu da dai sauransu.
Wanda asalin shirin yana fitowa ne ta kafar tashar youtube wanda bakori tv ke haskakawa a duk lokacin da sunka kamala daukar shirin, kuma anyi sa’a yana samun miliyoyin masu kallo.
To a yanzu shine daya daga cikin masu shirin din lawal ahamd ya fadi a shafinsa na sada zumunta wato Instagram kamar haka:
Instagram : Lawal Ahmad

Za’a fara haskaka shirin izzar so a tashoshin Dstv, Go tv, African magic hausa nan bada jimawa ba in sha Allah”.
Yanzu nan gaba shirin izzar so zai shiga cikin tagwayen shirye shirye da ake haskakawa a manyan tashoshi na tauraron dan adam irin kwana casain,dadin kowa,gidan badamasi da labarina.
Wanda shirin labarina za’a fara haskakashi a 2/7/2023 wanda kuma kamar yadda babban daraktan shirin ya bayyana yace za’a haskakashi har tashar youtube mai suna saira movies.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button