Uncategorized

Ni ‘Yar Asalin ƙabilar Igbo ce ~ Cewar Mawaƙiya Rihanna

Advertisment

Mawakiya Rihanna

Fitacciya kuma hamshaƙiyar attajiran wamawaƙiyar nan ta duniya Robyn Rihanna Fenty wadda aka fi sani da ‘Rihanna’ an haife ta a birnin Saint Michael ƙasar Barbados, amma yanzu ta bayyana cewa ita ƴar Africa ce.
Ta bayyana asalin nata ne a wani hira da aka yi da ita cikin wani Bidiyo kamar yadda Jaridun Republican News da Daily Times suka ruwaito.
Ta ce mahaifiyarta ta sanar da ita cewa ita ƴar asalin ƙabilar Igbo ce ma’ana Iyamura.
Rihanna

A cewarta, “Mahaifiya ta ta faɗa mini cewa ni ƴar asalin ƙabilar Igbo ce. Igbo ƙabila daga nahiyar Africa”.
HAUSA DAILY TIMES ta ruwaito a makon jiya mawakiyar na gina wani katafaren asibiti a ƙasar Malawi, inda aka ga Rihanna tana taimakawa Leburorin dake aikin gina asibitin da dakon ƙasa da ruwa.
Rihanna mai shekaru 33, mawaƙiya ce da ta yi fice a duniyar mawaƙa dake da zama a ƙasar Amurka.
Kafar watsa labaran FORBES na ƙasar Amurka a kamon jiya ta ayyana Rihanna a matsayin mawakiya mace mafi arziƙi a duniya da aka ƙiyasta kuɗin da ta mallaka da ƙimanin Dalar Amurka Biliyan Ɗaya da Miliyan ɗari bakwai wato ($1.7billion).
Baya ga waƙa, Rihanna hamshaƙiyar ƴar kasuwa ce a bangaren kwalliya (Fashion Business).

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button