Wata Sabuwa! Northern Hibiscuss Kalwancin Mata Zuwa Otal Ana Lalata Da Su — Bello Muhd Bello
A yanzu nan mun samu labari daga shafin fitacen jarumin masana’antar kannywood wanda dan asalin jos ne wato Bello Muhammad Bello BMB.
Inda ya nuna cewa kungiyar northern hibiscus babu wani aiki da suke bayan kai yan mata zuwa Abuja ko lagos otal otal.
Ga dai abinda ya fadi
“Da farko dai, wannan Shafin sune suke baiwa wata Kungiya ta mata masu sintirin zuwa Abuja da Lagos, suna yawo ofishi zuwa ofishi, otal zuwa otal suna harkar TALLATA JIKKUNANSU TA HANYAR BAYAR DA ABINDA ALLAH YA ALBARKACESU DA SHI NA DAGA NI’IMA DON SAMUN SUMA ABINDA SUKE NEMA A WAJEN MASU HANNU DA SHUNI KO LAUYOYIN KAMPANI KO MANAJOJIN KAFANI.
Ma’ana @nothern_.hibiscuss dai sun zama tamkar kawalai tsakanin wasu Matan Arewa da ‘Yan Kudancin Kasarnan.
Cikakken bayanin na nan a post din gaba…”