Kannywood

Ba zan auri Jahilin miji ba, cewar Jaruma Maimuna Muhd (wata Yarinya)

Fitacciyar jaruma a Masana’antar fina-finai ta Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da Maimuna Wata Yarinya, ta bayyana cewar, ita fa ba za ta auri namji jahili ba, don haka duk wanda za ta aure sai ta tantance shi, ta san ya na da ilimi da kuma tsoron Allah, yadda zai kiyaye mata mutuncin ta, da kuma na auren ta.

A tattaunawar da suka yi da wakilin jaridar Dimukaradiyya a Kano, Jarumar ta ce ” Ya kamata mu mata yan fim, mu yi wa kan mu fada, tun da mun san maza ga irin yadda su ke zuwa wajen mu, da wata manufa ta daban, don haka sai mu san namijin da za mu kula, don mace tana da daraja da mutunci kamar yadda Allah ya daukaka ta, don haka sai mu yi soyayya ta gaskiya idan namij ya zo ya ce yana son mu.” inji ta.

 

Maimuna Wata Yarinya

Kazalika ta kuma ce, “Ya kamata mu karance shi, mu ji daga ina ya zo? kuma da wacce manufa ya zo?” a cewar ta.

KARANTA WANNAN LABARIN:Ni ‘Yar Asalin ƙabilar Igbo ce ~ Cewar Mawaƙiya Rihanna
“Don matan da su ke harkar fim mun shahara da son kudi. Amma ni dai a ra’ayina zan fada maka ba zan auri duk namijin da ba shi da ilimi ba, wanda ya ke jahili ko dan iska, wanda bai san darajar mace ba, don haka kullum addu’a ta, Allah ya kawo mun namijin da ya san kima da darajar mace, a matsayin wanda zan aura” inji jarumar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button