Cibiyar Creative Helping Needy Foundation zasu Koyar Da Matasa 50 Sana’a Kyauta – Fauziyya D. Suleiman


A yau din nan ne shugabar creative helping neddy foundation ta fitar da wannan sanarwar koyawa matasa 50 Sana’a kyauta wanda an sanya ka’idoji ga masu son shiga cikin wannan tsari.
Ga abinda ta wallafa a shafin nata.
“DAMAR KOYA SANA’A GA MATASA 50
Kamar yadda mu ke ta kokarin ganin mun samarwa matasa aikin yi ga dama ta samu.
Gidauniyarmu ta @creativehelpingneddyfoundation ta yi hadin Gwiwa da Kamfanin Engausa Global Technologies, mun yunkuro domin koyawa matasa guda Hamsin(50) aikin yi irin na zamani domin zama da kafafunsu.
Abun da za a koyar da su ya hada da koyar da hada Solar da aikinta, Hada CCTV, koyar da gyaran wayoyi da sarrafasu, Sarrafa Kwanfuta da gyaranta, Sanya wayar Kariya mai wuta ta katanga, Sanya Tangaraho na ofisoshi(Intercom), Sanya tsaro na kofofi da sauransu.
A ka’idar abun da ake biya na kowanne Dalibi Naira Dubu Arba’in da Biyar ne(45k) na Ajin farko da Aji na biyu(advance class) tsahon Sati 11, amma saboda hadin Gwiwa za mu yi da Engausa kowanne Dalibi za mu biya (35k) yanzu.


Gidauniyarmu ta ware Naira Miiyan Biyu (2 millions) domin daukar nauyin koya karatun da kudin Alawus.
Za a dauki tsahon watanni Hudu ana koyawa matasan aiki har zuwa lokacin da za su kware.
Tsarin da za a bi domin amfana shine,
1. Matashi ya kasance yana da Sakamakon Sakandire 2. Shekaru Kar su wuce 18 zuwa 25. 3. Matashi ya kasance yana da katin Dankasa da lambar account. 5. Matashi ya kasance Maraya ne.
Akwai alawus na Naira Dubu daya da Dari biyar (1500) da za a dinga Baiwa Matashi duk sati domin kudin mota.
Daga ko’Ina matashi na da damar cin gajiyar shirin na tsahon watanni Hudu sai dai ku sani a Kano Makaranta ta ke ba za mu Baiwa kowa gurin kwana ba, wanda ya zo daga wata jaha zai nemi gurin kwanansa.
Ga Wanda ke bukatar shiga za su tura abubuwan da muka ambata a sama (Banda account no) ta lambar wayar da za mu Saka ko Adireshi na Email.
KA’IDOJI: Duk Wanda ya kira lambar Fauziyya D. Sulaiman ko ya mata what’sapp ko Dm ya fadi, Sai Dai a tuntubi lambar da za mu saka ko ta emeil.
Sannan Wanda aka tantance za a Kira su domin zuwa Interview, duk Wanda aka kira zai zo da takardun da aka bukata a sama na gaskiya (Original) domin tabbatar da shine.
Za a tuntubemu ta nan: email: [email protected].
Lambar waya: 07067336323.
Allah ya Sakawa masu taimakawa da alkairi, Kofa a Bude ta ke ga Wanda za su dauki nauyin Dalibai ko nawa ne, Rijista Dai 45k ga kowanne Dalibi.”
Ga kuma bidiyo nan domin saurare daga bakin shugabar wannan kungiya.
