Kannywood

Wasu Abubuwan da Ya kamata Ku sani kan Zainab Booth Mahaifiyar Maryam Booth

Kannywood Ta Girgiza Da Rasuwar Jaruma Zainab Booth. Inda Suketa Nuna Alhinin Su, Ga Wasu Abubuwa Daya Kamata Ku Sani Dangane Da Jarumar.

‘Yar wasan fina-finan Kannywood, Hajiya Zainab Booth, wadda ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ta rasu ne a birnin Kano da daren Alhamis, a cewar danta Umar Booth, a tattaunawarsa da BBC.

Ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, hakika Allah cikin ikonsa ya yi wa mahaifiyarmu Hajiya Zainab Booth rasuwa bayan fama da rashin lafiya, ta rasu a daren Alhamis da misalin karshe 9 na dare, za a yi jana’izarta a yau Juma’a idan Allah ya kai mu.

BUDA WANNAN :

Innalillahi Maganar Karshe Da Marigayiya zainab Booth Mahaifiyar Maryam Booth kafin ta Rasu

Ta rasu ta bar ‘ya’ya hudu, maza biyu da mata biyu, wato Ni Umar, sai Amude da Maryam da kuma Sadiya, sai jikoki guda biyu,” in ji Umar.

Umar ya kara da cewa za a tuna da Hajiya Zainab Booth da son zumunci da yawan yin addu’a, sannan ita din uwa ce ga kowa don haka ne ma duk inda ta shiga za ka ji ana kiranta Mama, Mama.

A kwanakin baya ne dai marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda ‘yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.

DUBA WANNAN
Bidiyo: Jana’izar Zainab Booth Uwar Maryam Booth wacce ta rasu a jiya Alhamis a Kano

Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da ‘ya’yanta uku suka kasance su ma taurari.

An yi jana’izarta a gidanta da ke birnin Kano da misalin karfe takwas na safiyar Juma’a.

Kannywood ta fada halin alhini

Tuni dai taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood suka soma alhinin rasuwar Hajiya Zainab Booth.

Taurari da furodusoshi da saura masu ruwa da tsaki irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi da Aminu Saira sun yi addu’ar Allah ya jikanta.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Aminu Saira ya yi mata addu’a kamar haka:

“Allah ya jikan ki da Rahama Hajiya Zainab, Allah ya yafe kura-kuran ki, Allah ya sa aljannah ta zama makomar ki”

Shi ma Ali Nuhu cewa ya yi: “Innalillahi wa inna ilahir raj’un, ALLAH ya yi wa Haj Zainab Musa Booth rasuwa, gobe za a yi jana’iza a gidan ta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road da karfe takwas na safe (8:00am). ALLAH ya jikanta da rahama, ya sa aljanna ce makomarta, amin.”

A nata bangaren, Saratu Gidado wacce aka fi sani Daso ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar:

“Allahu Akbar. Allah yayiwa Abokiyar Sana’ar mu ta FILM rasuwa wato Zainab Booth. Yau Alhamis 01/07/2021. Muna mika sakon Ta’aziyar mu ga Iyalinta. Allah ya yafe mata kurakurenta. @officialmaryambooth”.


Sauran Manya Da Kananan Jarumai Suma Sun Nuna Alhininsu, Inda Su Mika Ta’aziyyarsu Ta Hanyar Bugo Waya Da Tura Sakonnin Karta Kwana Da Kuma Shoshiyal Midiya.
@BBCHausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button