Hausa Series FimKannywood

Shirin wasannin Kwaikwayo na “A Duniya” da “Haram” ba sa koyar da komai sai miyagun halaye – Sanusi Bature

Advertisment

Sanusi Bature

Tsohon mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019, Abba Kabir Yusuf wato Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa matuƙar hukumar tace fina-finai ta jihar Kanon da gaske ta ke akan ayyukanta to ya kamata ta dakatar da haska shirin wasan kwaikwayon nan guda biyu masu dogon zango wato “A Duniya” da kuma “Haram”
Shirin Fim din A Duniya kenan

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa hakan ne a shafinsa na facebook, cikin harshen Ingilishi a safiyar yau Lahadi.
“Idan har da gaske hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ke yi akan ayyukanta to ya kamata ta dakatar da shirin wasan kwaikwayo na “A Duniya” da kuma “Haram” domin suna matuƙar kawo illa a cikin al’ummar mu”
Ya ƙara da cewa wasannin ba sa koyar da komai illa miyagun halaye da yanzu haka al’umma ke fama da su daga ɓata garin matasa.
“Waɗannan fina–finan ba sa koyar da komai sai ƙara koyar da mugayen halayen da mu ke fama da su, da su ka haɗa da Daba da Ƙwacen waya da Shaye – shayen miyagun kwayoyi da kuma Safarar yara ƙanana wanda hakan ke cutar da al’umma”
Haka kuma Sanusi Baturen ya zargi hukumar ta tace fina-finai da yin bita da ƙulli ga waɗanda su ke adawa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, inda ta ke huce fushinta akan su.
Shirin Fim Din Haram

“Ina mamakin yadda hukumar tace fina-finan ta fi mayar da hankalin ido rufe akan masu adawa da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ke cikin masana’antar Kanywood” In ji Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sai dai hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba Afakkallah, ya ce hukumarsa ba za ta saurarawa duk wani dan fim ko mawaki ba matukar ya sabawa dokar da ta kafa hukumar ta shekarar 2001.
©Labarai-24

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button