Kannywood

Bana Rubuta Waƙokina A kai Nake Rerawa ~ Ado Gwanja

Fitaccen mawakin nan na Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finan Kannywood Ado Gwanja ya ce ya rera kusan wakoki 600 tun da ya soma sana’arsa ta waka kuma galibinsu da ka ya rera su.

Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa Instagram Live ranar Alhamis.
Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce “gaskiya babu abin da yae ba ni wahala” idan ya zo rera waka.
“Ina kiran mai kida na ce ‘buga min kida yanayi kaza, ko yanayi kaza’, sai a yi min kida sikeleton…ina cikin ji wakar za ta zo. Idan ta zo sai na ce ‘samo min furodusoshi,” a cewar Ado Gwanja.
Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu sun ba shi shawarar yin hakan.

Ya ce wakar da ya soma yi ita ce Gawasa “kuma da na yi ta ni kadai aka bari na yi ta jin kaya ta. Na ji kayata ta ishe ni, na kuna mnata inda na ajiye ta”.
Wakokinsa da dama sun yi tashe musamman Kujerar Tsakar Gida, Asha Rawa, da Salon Kida.
Mawakin ya ce baya ga sana’ar waka, babu sana’ar da yake so kamar ta shayi.
“Saboda mu asali a gidanmu – ko mace ko namiji, har iyayenmu da sana’ar shayi aka auro su,’ in ji Ado Gwanja.
Ado Gwanja ya ce ya daina fitowa a matsayin dan daudu a fina-finan Kanyywood saboda “na fi so matata ta dan yi dariyarta ta fadi ta tashi daga ni sai ita.”
A baya dai ya shaida wa BBC Hausa cewa tsabar
yadda ya iya kwaikwayon ‘yan daudu ne ya sa ake sa shi a fim din da ya danganci haka.
Wannan layi ne

Wane ne Ado Gwanja?

  • Dan asalin unguwar Kofar Wambai ce ta Kano
  • Mahaifinsa shahararren mai shayi ne da ak fi sani da Gadagi Mai Shayi
  • Ya yi karatu har zuwa sakandare
  • Yana da mace daya da ‘ya daya
  • Ya kan fito a fim kuma yana waka
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button