Kannywood

Hukumar Tace Fina-finai Ta Gayyaci Ado Gwanja Don Tuhumar Sa Kan Waƙar CHASS

Wani lauya a jihar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya yi barazanar maka Hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban kotu, matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin nan, Ado Isa Gwanja, daga fitar da wata sabuwar waka da ya yi mai taken “Asosa

Barr. Gandu, wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu daceba acikin waƙoƙinsa, ya nuna cewa barin irin waɗannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.

Lauyan ya ce, kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta ɗauki mawakin aiki a karkashin hukumar Hisbah domin yin amfani da hikimarsa wajen faɗakar da al’umma saɓanin yadda ya ke amfani da hikimar ta wata hanya daban.

A ƙarshe, lauyan ya jaddada barazanar maka hukumar Hisbah agaban kotu matukar ta haura kwana uku bata dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar waƙar ba

Wanda daga karshe dai hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta aika da takarda gayyata ga mawakin Ado Gwanja akan sabuwar wakarsa da ya fitasa mai suna ‘Chass Asosa‘.

Wanda gidan rediyon freedom radio sun zanta da shugaban hukumar tace finafinai Isma’il afakallahu inda yake cewa.

A duk lokacin da ka fitar da wani abu da zai taba mutuncin al’umma addini su ko al’adarsu babu wanda zai ce maka mai kyau ne ko marar kyau ne dai sai hukuma.

Saboda haka ne aka samar da wadannan hukumomi kuma tuni mun turamasa goron gayyata domi yazo nan hukuma muga yadda za’a daƙile irin wadannan abubuwa irin wakokin da ake fitar ba bisa sa hannun hukuma ba ko sanya kalamai wadanda basu daci na taba tarbiyar mutane.”

Ga sautin hirar nan domin ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button