Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma Na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari


Iyalan shugaban kasa Buhari sun kai lefen Zarah Bayero masarautar Kano ta dabo
Kamar yadda aka gano, a cikin lefen akwai akwatuna 3 na zinari da lu’u-lu’u
Har ila yau, an samu wasu akwatuna 2 dankare da tsabar kudi daga iyalan Buhari
Masarautar Kano
Labarai da dumi dake zuwa ma Legit.ng shine na kai gagarumin Lefen auren Yusuf Buhari, da namiji daya tilo ga shugaban kasa Buhari da aka yi masarautar Kano.
Neman aure
Tuni dai Legit.ng ta ruwaito yadda aka je neman auren Gimbiya Zarah Bayero karkashin shugabancin gwamna Badaru na jihar Jigawa inda tawagar ta cika da wasu gwamnoni, ministoci da kuma kusoshin gwamnati.
An gano cewa bayan babbar sallah Yusuf Buhari zai angwance da tsuleliyar Gimbiya, Zarah Bayero, diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Bayero.
An kai lefe
Tuni dai shirye-shirye suka kankama tunda a ranar Alhamis iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari suka dira birnin dabo dauke da lefen alfarma.
Kamar yadda wasni shafi mai suna @arewafamilyweddings ya wallafa a Instagram, ya tabbatar da cewa an mika lefen masarautar Kano.
View this post on Instagram
Kamar yadda wallafar ta zo, “Muna taya Gimbiyarmu murna. Kudi sun yi. Duba akwatuna 3 cike da zinarai da lu’u-lu’u da kuma akwatuna biyu dankare da tsabar kudi daga iyalan shugaban kasa.”
Ba wannan shafin kadai ya wallafa labarin lefen ba, shafin gidan sirikan Zarah Buhari, mai amfani da suna @keepingupwiththeindimis.
Shafin ya taya Yusuf Buhari murna inda ya kara jaddada cewa an kai lefen masarautar Kano.Tattara wannan bayyani daga legit
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




