Na zo Najeriya bani da ko dinare ɗaya amma yanzu ni multi- biloniya ce- In Hadiza Gabon




Hadiza Aliyu Gabon yar shekara 32 a duniya. An haifeta a ranar 19 ga watan June 1989 a Libreville babban birnin Gabos. Ta yi karantun Diploma a harshe faransanci a Higher Institution based a Gabon.
Kamar yadda jaridar Mikiya na ruwaito.Bayan ta karɓi takardar diploma a shekarar 2006. Ta yanke shawarar zuwa Najeriya jihar Kaduna a shekarar 2007 domin ta cigaba da karatu, ta zauna a gidan wata yayarta da ta ke aure.
Bayan wani loƙaci sai ta ji tana sha’awar shiga shirin fina-finai saidai a wancan loƙacin bata jin Hausa ko turanci


Daga baya, ta yanke shawarar tunkarar sarkin kannywood Ali Nuhu domin ya taimaka mata shiga harkar fina-finai a masa’antar Kannywood. Daga nan ne ta fara jan zaranta a fina-finan Hausa.
Yanzu haka Hadiza Gabon tana ɗaya daga cikin manyan jarumai a masa’antar kannywood sannan tana sahun waɗanda su ka mallaki biliyoyin daloli ta sanadiyar film
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.





