Yadda annobar Spanish Flu Ta Yi barna a Nigeria shekara 100 Da Ta wuce
Shekaru 100 da suka gabata ne duniya ta yi fama da mummunar annobar cutar da ake kira Spanish Flu wacce rahotanni suka ce ta kashe mutum miliyan 50.
Annobar ta yi mummunar illa kan al’ummomin da dama tuni yakin duniya na farko ya daidaita.
An yi amannar sai da kashi uku cikin hudu na al’ummar duniya suka kamu sannan mutum miliyan 50 ta kashe a fadin duniya.
Duk da cewa sunan cutar Spanish Flu ba daga kasar Sifaniya ta samo asali ba. Ta samu wannan sunan ne saboda jaridun Sifaniya ne suka fara ruwaito labarin barkewarta.
Wannan cuta wacce ta shafe shakara biyu tana addabar duniya tun daga 1918 har zuwa 1920, ta shafi kusan dukkan kasashen duniya da suka hada da Najeriya.
Farfesa Abdussalam Nasidi, tsohon shugaban Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC, ya shaida wa BBC cewa, ”Kuma ta shiga har Najeriya da ma arewa.
A lokacin da annobar ta barke yawan al’ummar Najeriya ya haura miliyan takwas da dubu 600, kuma mutum 199,325 ne suka mutu.
”Annobar ta kai wata shida tana addabar mutane kuma ta yi ta yaduwa ne ta hanyar shiga da fitar da aka dinga yi tsakanin kasashe ta jirgin ruwa, abin da ya zama sanadin yaduwarta a duniya,” in ji Farfesa Nasidi.
Rahotanni sun ce annobar Spanish Flu ta kashe mutum 57,978 a jihar Kano kawai, jihar da yawan mutanenta ya haura miliyan biyu da dubu 700 ne kawai a wancan lokacin.
A lokacin da annobar ta addabi duniya babu ci gaban kimiyya kamar yanzu don haka an sha wahala wajen dakile ta.
#bbchausa