Labarai

Buhari Ya Nemi Kara Wa’adin Aje Aikin Malaman Makaranta Zuwa Shekara 65


Shugaba Buhari. Photo: @BashirAhmad

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya aike da wata wasika ya zuwa majalissar dattawa inda yake rokonsu da su tabbatar da kara wa’adin aje aikin malaman makaranta daga shekara 60 zuwa 65.
Haka nan ma shugaban ya bukaci a kara tsawon lokacin aiki daga shekaru 35 zuwa 40.
Jaridar arewamobile ta ruwaito cewa rokon yana zuwa ne a daidai lokacin da Buhari ya aike da sunan manjo janaral Farouk Yahaya don tabbatarwa a matsayin sabon shugaban sojoji na kasa.
Shugaban ya bayyana cewa wannan yunkuri na karin wa’adin aiki ga malamai na kan tsarin sashi na 58 shafi na 2 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button