Labarai

Yanzu – Yanzu :Khalifa Sheikh Mahi Inyass Ya Nada Sarkin Kano Muhammadu Sunusi || Halifan Tijjaniyya A Najeriya

A daren yau Khalifa Sheikh Mahi Inyass ya bayyana nadin Halifancin Muhammadu Sunusi ||. Ga jawabin nadin kamar yanda aka wallafa a shafin Facebook na Khalifa Sheikh Mahi Inyass RTA
فليعلم الجميع وليناد المنادي بأن أهل الحل والعقد والقول النافذ فى الفيضة التجانية، ألا وهو الخليفة العام للفيضة الشيخ محمد الماحي إبراهيم نياس توج أمير كانو السابق محمد سنوسي لاميطو سنوسي خليفة للتجانية رسميا فى نيجيريا.
وعلى هذا القضاء النافذ، نتضرع للمولى سائلين إياه أن يؤيده على تحمل المسؤلية وأداءها كما يتوقع أو أكثر إنه ولي ذلك والقادر عليه.
# أبوبكر سرنبي إبراهيم غوث الفيضي
Fassara jawabin :
Muna sanr da kowa, kuma duk mai kira yayi kira cewa ma’abocin kullawa da warwarewa da zartarwa a cikin sha’anin faidhar tijjaniyya, wanda shine Khalifa Sheikh Mahi Inyass RTA ya nada tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi halifan tijjaniyya a Najeriya.

Mahi Inyass tare da Sanusi Lamido sanusi II kenan

A bisa wannan zartarwar, muna rokon ubangiji cikin kankar da kai da ya karfafe shi bisa daukan wannan nauyin da aka daura masa, kuma ya aiwatar da ita kamar yanda akayi tsammani ko fiye da haka.
Mai jawabi : Abubakar Sirrin Baye Inyass.
Anyi wannan nadin ne a daren yau bayan addu’ar khatmar Alqur’ani da ya gabata a Kaulaha inda Khalifa Muhammadu Sunusi || ya samu halarta.majiyarmu ta dauko wannan rubutu daga shafin darikar tijjaniya mai suna Fityanul Islam of Nigeria

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button