Yanzu – Yanzu : Jamhuriyyar Benin ta saki Sunday Ighoho
Gwamnatin Benin ta saki jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya Sunday Ighoho.
An saki Ighoho domin ba shi damar zuwa ganin likita a asibiti bisa sharaɗin cewa ba zai bar asibiti ba ko Cotonou saboda wani dalili, kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyinsa Yomi Aliyu, ya tabbatar wa .
Ya ce Farfesa Wole Soyinkaɗaya daga cikin shugabannin Yarbawa ya taimaka aka Sunday Ighoho domin zuwa asibiti.
A watan Yulin 2021 aka kama Sunday Ighoho mai da’awar kafa ƙasar Yarbawa ta Oduduwa.
Ana tuhumarsa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, da laifin shiga kasar ba bisa ka’ida ba tare da kokarin tayar da husuma, amma ya musanta hakan.
Igboho ya tsere ne daga Najeriya ya tsallaka Benin bayan samamen da ‘yan sanda suka kai gidansa a farkon watan Yulin 2021, inda aka kashe biyu daga cikin yaransa.
Sources: Bbchausa