Kannywood

Dalilin Rabuwar Auren Sani Musa Danja Da Mansurah Isah – Fim magazine

Fitacciyar jaruma Mansurah Isah ta daɗe da tarewa a gidan hayar da ta kama a Kano bayan tsinkewar igiyar auren ta da Sani Musa Danja, wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim a yau.
Labarin da ake yaɗawa cewa auren jaruman biyu na Kannywood ya mutu ya na ci gaba da bazuwa a tsakanin ‘yan fim da sauran jama’ar gari, amma dai su jaruman sun ƙi cewa uffan a kai.
Shirun da su ka yi ya ƙara iza wutar ji-ta-ji-tar.
Tsofaffin jaruman dai sun yi aure ne a cikin 2007, kuma sun haifi ‘ya’ya biyar – mace biyu (Khadijatul Iman da Riqzat da maza uku (Khalifa Sani, Yakubu da Yusuf).
A ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa, an ce wai Mansurah ta wallafa wani saƙo a Instagram jiya da dare, inda ta bayyana cewa a yanzu babu aure tsakanin ta da Sani.
An ce bayan minti ɗaya sai ta goge rubutun ba tare da ta bada dalili ba.
Sai dai kuma mujallar Fim ta tambayi ‘yan fim da dama su nuna mata hoton saƙon da aka ce ta wallafa ɗin, wato ‘screenshot’, amma babu wanda ya ke da shi.
Karanta kuma Ɗabi’a: A daina yi wa ‘yan Kannywood jama’u – Maigarin ‘Daɗin Kowa’
Labarin mutuwar auren ya haifar da surutai a guruf-guruf na ‘yan fim da kuma wasu wurare na soshiyal midiya tun daga jiyan.
Mujallar Fim ta so jin ƙarin bayani ta bakin jaruman biyu, amma ba su amsa waya ba. Haka kuma ba su amsa saƙon tes da mujallar ta tura musu na neman gaskiyar labarin ba.
Wata majiya ta kurkusa da Mansurah ta shaida wa mujallar Fim cewa auren ya jima da mutuwa, kawai faɗa ne ba a yi ba.
“Auren Sani da Mansurah Isah ya daɗe da mutuwa. Har Mansurah ma ta kwashe kayan ta daga gidan Sani, ta koma gidan hayar da ta kama,” inji majiyar. “Sun riƙa nuna wa mutane kamar su na tare.”
Majiyar ta ƙara da cewa Mansurah ta koma gidan ne tare da ‘ya’yan ta, kuma ta sha alwashin ba za ta taɓa ba Sani ɗan ta ya riƙa ba.
Wata majiyar ta daban kuma ta sanar da wakilin mu cewa auren tsohuwar jarumar da fitaccen jarumar ya girgiza ne lokacin da ya ƙara aure.
Karanta kuma Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga ‘yan fim
Majiyar ta ce, “Shakka babu, Sani ya yi aure a asirce a Kaduna, kuma matar ma ta haifi ɗa namiji.”
Ta ƙara da cewa Mansurah ba ta san da auren ba har zuwa lokacin da aka yi haihuwar.
To amma binciken da Fim ta yi a Kaduna bai samu tabbacin wannan auren da aka ce Sani ya yi ba.
An faɗa wa wannan mujallar cewa ba wannan ba ne karo na farko da Sani ya saki Mansurah.
“Ya taɓa sakin ta a lokacin da su ke zaune a unguwar Karu a Abuja, daga baya aka sasanta su,” inji mai ba mu labarin.
Mai ba mu labarin ta ce Mansurah ta gaji da halayen Sani ne na rashin kula da iyali. “Ita ke komai a gidan, har da ciyarwa,” inji majiyar. “Mansurah mace ce mai ƙoƙarin neman abin rufa wa kan ta da iyalin ta asiri.”
Wakilin mu ya lura da cewa jaruman biyu kan wallafa hotunan su tare da ‘ya’yan su a soshiyal midiya a lokacin bukukuwan Sallah, amma a bana ba su yi hakan ba. Mansurah ta wallafa hotunan ‘ya’yan ne su kaɗai, shi kuma Sani ya wallafa hotunan da ya ɗauka shi da abokin sa Yakubu Muhammad da kuma ‘ya’yan a ranar Sallah.
Karanta kuma Saura ƙiris na yi wuf da wani, inji Hauwa Waraka
Rabon da Mansurah ta wallafa hotunan mijin nata tun cikin Janairu 2021 lokacin da ta tura hotunan sa na tallar kamfanin Maggi. Ita jakada ce ta kamfanin, inda biyan ta maƙudan kuɗaɗe.
Mansurah dai ta na ci gaba da aikin ta na tallafa wa mabuƙata a ƙarƙashin gidauniyar ta mai suna ‘Today’s Life Foundation’.
Mutuwar auren ta ta nuna cewa ‘tagwayen’ kamfanin 2-Effects Empire, wato Sani Danja da jarumi Yakubu Muhammad, duk sun rabu da matan su da su ka wanka a auren fari.
Yakubu ya shafe shekaru masu yawa tun da ya saki Sadiya, ɗiyar fitacciyar jaruma Hajiya Zainab Musa Booth kuma yayar jaruma Maryam Booth.
Sun haifi ‘ya ɗaya mai suna Nadiya, kuma har yanzu Yakubu bai yi wani auren ba.
wannan labarin mun dauko shi ne daga fim magazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button