Shin Da Gaske Ne Nazir M Ahmad (Sarkin Waka) Ya Koma Tafiyar PDP?
INA YA DOSA?
A cikin makon nan ne Fitaccen Mawaki Nazir Muhammad Ahmad, wanda ake yi wa lakabi da Naziru Sarkin Waka ya saki wani sabon bidiyon wakar da ya yi wa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wadda ya sanyawa suna BABA DA BABA. Wakar ya yi ta ne domin taya shi Gandujen yakin neman zabe na tazarcen da ya ke nema. Tun bayan lokacin da mawakin ya saki wakar ta sa ya ci gaba da arangama da zagi na batanci gami da munanan kalamai ga mabiyan sa na instagram, har ma wasu masoyan suka rika yin Tir! tare da yin Allah wadai da mawakin sanadiyyar tafiyar Ganduje da ya ke ciki, wadda suke ganin sam tafiyar ba ta dace da shi ba.
Wani abun mamaki game da mawakin, a jiya kuma sai aka nemi wakar aka rasa a shafin mawakin, wanda alamu ke nuni da cewa ya goge wakar da ya yi wa Gandujen, kwatsam sai aka ga har ma ya yi wani dan karamin bidiyo ya saki a shafin sa na Instagram mai taken ‘BABU RUWAN SARKI DA $DOLA. Inda a karshe ya bayyana cewa shi ma ‘ya’yan sa ABBA suke kiran sa.
A daren yau, wanda ya rage sa’oi kadan a yi zaben Gwamnoni, an ga mawakin tare da wasu ‘yan fim sun ziyarci dan takarar gwamnan jihar Kano na Jam’iyyar adawa ta PDP wato Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) har ma suka yi hotuna tare, sannan mawakin ya rataya Tutar jam’iyyar PDP irin wadda ake ba wakilan rumfa na zaben da za a yi gobe.
Sai dai wasu na ganin daman mawakin yana daya daga cikin wadanda za su yi shinkafa da wake a zaben bana, wato a sama Buhari, a kasa kuma sai sun darje, Abun tambaya a nan shi ne, shin mawakin ya ci banza kenan tun da ya riga ya kammala kwangilar wakar da aka ba shi? © Kannywood Exclusive
07-03-2019