Rabuwar Mu Da Sani Danja shine Yafi Dacewa – cewar Mansurah Isah
MANSURAH Isah ta bayyana cewa mutuwar auren ta da Sani Musa Danja ita ce ta fi dacewa da rayuwar su.
Ta ce Sani Danja “ya na buƙatar ya ci gaba da gudanar da rayuwar sa, kuma ni ma ina buƙatar in ci gaba da gudanar tawa rayuwar.”
Kamar yadda fimmagazine na ruwaito. Mansurah ta bada haƙuri ga duk wanda bai ji daɗin mutuwar auren ba, to amma “abin da ya fi dacewa mu yi kenan.”
Mansurah ta yi waɗannan kalaman ne a rubutun da ta yi a Instagram jiya inda ta bayyana labarin mutuwar auren, rubutun da yanzu mujallar Fim ta samo shi.
Idan kun tuna, a labarin mutuwar auren jaruman biyu na Kannywood wanda mu ka wallafa a daren jiya, mun faɗa muku cewa babu wanda ya nuna mana hoton rubutun da aka ce tsohuwar jarumar ta yi a Instagram inda ta bayyana cewa auren ya mutu.
A labarin, mun kuma bayyana cewa Mansurah ta goge rubutun jim kaɗan bayan da ta wallafa shi, amma ba ta faɗi dalili ba.
Karanta kuma Jarumar Kannywood, Khadija Abubakar Mahmud, ta rasu
Ta goge rubutun ne bayan minti 4 kacal da tura shi.
To, bayan mun saki labarin ya yaɗu a cikin miliyoyin mutane, ɗazu sai wani makarancin mujallar ya faɗa wa wakilin mu cewa ai shi ya samu ɗaukar hoton rubutun da Mansurar ta yi kafin ta goge shi.
Wakilin namu ya buƙaci ya turo masa ya gani, shi kuma ya yi hakan.
Tsohuwar jarumar ta yi rubutun ne da Turanci, sannan ta haɗa da hoton ta tare da Sani Danja.
Ga abin da ta rubuta kamar yadda mujallar Fim ta fassara shi:
“Ku yi haƙuri da kunyar da mu ka ba ku, masoyan mu da abokan mu da iyalan mu.
“Ni da Sani Danja ba mu tare yanzu.
Rubutun Mansurah Isah kan mutuwar auren ta, wanda ta goge bayan minti 4 da tura shi
“Ba mu so mu ɓata wa kowa rai amma wannan rayuwar mu ce kuma shawarar da mu ka yanke wa kan mu kenan. Mu na so kowa ya mutunta ta, saboda mun san abin da hakan ke ciki kafin mutum ya ɗauki irin wannan matakin.
“Har yanzu mu na kula da junan mu tare da mara wa junan mu baya. Amma dai mu na ganin abin da ya fi dacewa mu yi kenan.
“Ya na buƙatar ya ci gaba da gudanar da rayuwar sa, kuma ni ma ina buƙatar in ci gaba da gudanar tawa rayuwar.
“Mun gode da fahimtar ku.”
Wata mijiya ta shaida wa mujallar Fim cewa Mansurah ta kama gida ne a bayan gidan tsohon mijin nata da ke unguwar Giginyu.
A yanzu dai mutane na ta bayyana alhini da mamaki kan mutuwar wannan aure, inda da dama su ke baƙin cikin abin da ya faru.
“Sani da Mansurah sun dace da juna wallahi, ga yaran su gwanin ban sha’awa. Ban taɓa zaton za a wayi gari a ce sun rabu ba,” inji wata mai karatun mujallar Fim.
Wani manazarcin al’amuran yau da kullum kuma ya ce: “Zan so a ce sun shirya, domin da su ne mu ke kafa misali na ɗorewar auren ‘yan fim.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ba wannan ba ne karo na farko da jarumar su ka rabu, domin kuwa Sani ya taɓa sakin Mansurah lokacin su na zaune a Abuja a zamanin gwamnatin Jonathan.