Sheikh Dr Ahmad Gumi Ya Fadi Dalilin Da Yasa Ake Kokarin YaƘarsa


Malam ya fara da kawo tarihin wasu ‘yan ta’adda, khawarijawan da sukayi zamani da su Ibnul Qayyumul Jawziyyah da Sheikhul Islam Ahmad Abdul-Haleem Ibn Taimiyyah Al-harraniy wanda ake kira da Mogul da Tatar
Musulmai ne suka lalace a lokacin, sai Allah Ya kawo ‘yan ta’addan Tatar da Mogul wanda suke rayuwa cikin daji, mutane ne basu san komai ba sai hawa dawaki suka shigo cikin Musulmi da fushi sukayi kaca-kaca da Musulmi a Baghdad, suka shiga har fadar Khalifan Musulunci na lokacin suka yanka suka kashe Musulmi, suka rusa Baghdad suka shiga Palasdin, sojan Misrah su suka tsirar da Musulmai
Dr Ahmad Mahmud Gumi yaci gaba da cewa; to amma daga baya kun san me ya faru? sai ‘yan ta’addan Tatar suka fahimci Musulunci suka Musulunta, da Tatar suka fahimci Musulunci sai suka yada addinin Musuluncin har Kasar India shekara kusan dubu daya suna shugabancin Musulunci a India
Wato kunga kenan Allah Ya turo mana mutane jahilai ya azabtar da mu, sannan daga baya suka fahimci Musulunci
Don haka fulani makiyayan nan da kuke gani kunga ana basu Littafi ko? to ba abin mamaki bane nan gaba su zo su zama Malamanku, domin rashin sani ne, amma kamar yadda fulanin jejin nan suke da kwazo da rashin tsoro da dukufa akan abu, idan sun fahimci addini ba zasu zama kamar mu ba, inji Dr Ahmad Gumi
Malamin yaci gaba da cewa; to shiyasa wasu miyagun mutane ke tsoron mu kaiwa fulanin jeji masu garkuwa da mutane da’awar addinin Musulunci, shiyasa hankalin makiya Musulunci yayi iyakar tashi da suka ga muna kaiwa barayin daji Littafi su koyi addinin Musulunci ba addinin ta’addanci ba, muna kiransu su bar sata, su bar zina, su bar shaye-shaye, su bar fyade, su bautawa Allah, shine abinda muke kai musu, sannan kada su yarda da wata kungiyar addini, suyi Musulunci kawai
Wannan ne babban dalilin da yasa hankalin makiya Musulunci ya tashi, duk yadda za’ayi wannan tafiyar da mukeyi sai sun lalata ta, inji Dr Ahmad Gumi
Kunga Zamfara an samu zaman lafiya, amma yau mun wayi gari an kama yara a Jangebe, nayi magana da Gwamnan Zamfara da wasu shugabannin Fulani sunce wadansu tsiraru ne wadanda duk sulhun da ake kokaron yi basa so, sunki yadda, sune suka kwashe yaran
Amma duk wanda akayi sulhu dashi gaba daya kakaf bai shiga cikin wannan aikin ba, kuma sune yanzu ma suke neman hanyar da zasu kwato yaran, tsakani da Allah sulhu na da amfani ko bai dashi? to amma ana su a nunawa mutane cewa sulhu bai da amfani, sai dai wuta da bakin bindiga, inji Sheikh Dr Ahmad Gumi
Allah Ka tsare mana Malam Dr Ahmad Gumi, Allah Ka bashi kariya daga cutarwan makiya Musulunci da munafukai, Allah Ka bashi nasara Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum Datti Assalafy ne ya wallafa Wannan shafinsa


